Yau saura kimanin shekaru 20 a cika karnin guda cif (shekaru 100) da karya lagon zaluncin amfani da yaki wajen mulkar mutane a doron kasa. Ba ina nufin ba a yaki a ko ina a cikin duniya ba a halin yanzu, har yanzu akwai wuraren da suke fama, ina nufin yaki mai gamewa irin wanda aka gwabza a yakin duniya na biyu wanda kasar Sin ta fafata da Japan, sauran sassan duniya suka fafata da Jamus da Italiya.
Duniya ta yi sabon zubi bayan cin nasarar yakin duniya na biyu, inda ya kai ga kafuwar Majalisar Dinkin Duniya domin samar da ’yanci da maslaha ga rayuwar bil’adama. An yi hakan ne da nufin bude hanyoyin samun ci gaba ta yadda duniya za ta yi dadin zama ba kawai ga mutane ba har da sauran halittun doron kasa. Wannan nasara ce babba, domin tana nuna al’ummar duniya sun dauki darasi daga kazamin yakin da ya salwantar da miliyoyin rayukan jama’a da kuma nuna wa duk wani mai mulkin kama-karya cewa zamanin cin karensa babu babbaka ya kare.
Sai dai kuma kash! A wannan karni na 21 da muke ciki, akwai masu kokarin sake maido da hannun agogo baya bisa barazanar sake maido da zamanin kauyanci na amfani da yaki domin “wai cimma muradu na kashin kai”. A makon da ya gabata, Amurka ta sake wa ma’aikatar tsaronta suna zuwa “Ma’aikatar Yaki” a karkashin wata dokar bangaren zartaswa wadda a karkashinta, kasar ta ce a shirye take ta tsunduma yaki don kare muradunta.
Ya kamata kasar ta fahimci cewa, mutanen zamanin nan suna da wayewa irin ta karnin da suke rayuwa a ciki. Yaki ba zai taba samar da nasara mai dorewa ba a zamanin nan. Kuma ita ce ma ya kamata ta fi kowa fahimtar hakan, domin ta gwabza a Afghanistan babu nasara, ta afka wa Iraki ba ta ci riba ba illa asara. Haka nan sauran wurare da ake ta nuna mata yatsa bisa tayar da fitina irin su Libiya har yau al’amura sun kasa daidaita yadda take muradi.
Ya kamata duk wata kasa da take nufin duniya da alheri a wannan zamanin, ta mayar da akalarta ga hanyoyin samun ci gaba da bunkasa cikin lumana. Karni na 21, karni ne da ilimi ya habaka sosai a duniya. Ta ko ina idan an duba za a ga yadda ake samun ci gaba a bangaren kimiyya da fasaha, da tattalin arziki da kuma wayewar kai da cudanyar jama’a. Duniya ta zamo dunkulalliya ta yadda wanda yake mahudar rana da mafadarta ba su yi nesa da juna ba.
Duk kasar da take son kawo wa al’ummarta ci gaba ta wayewar zamanin da muke ciki wajibi ne ta mayar da hankali a kan gwada basirar ilimin kirkiro da sabbin fasahohi na ci gaba wadda hatta sauran al’ummomi za su amfana, amma ba tayar da husuma da neman zubar da jini ko mai karfi ya danne mara karfi ba. Gudanar da gasa mai tsafta a ko wane fage na ci gaba halas ne, saboda hakan na samar da karin kuzarin ci gaba, amma ba komawa ga zamanin kauyanci na rayuwa tamkar ta namun daji ba! (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp