Tun daga gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008 zuwa gasar wasannin Asiya ta Guangzhou ta shekarar 2010, haka nan daga gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na shekarar 2022 zuwa gasar wasannin Asiya ta Hangzhou ta shekarar 2023, da kuma gasar wasannin hunturu ta Asiya ta shekarar 2025 da ba a jima da kammalawa ba, kasar Sin ta nuna bajinta wajen kara kaimin bunkasa wasannin motsa jiki na Olympics.
Shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya, Thomas Bach ya bayyana hakan a kwanan baya, a wata hira da wakiliyar babban rukunin gidajen yada labarai na kasar Sin, inda ya kara da cewa, kasar Sin ta ba da gagarumar gudummawa wajen raya harkar wasannin Olympics.
- Ministan Wajen Sin Ya Yi Kiran Hadin Gwiwar Kasashen G20 Don Gina Duniya Mai Adalci Da Ci Gaba Na Bai-daya
- Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince Da Kwangilar Aiki Da NAHCON Bayan Sabunta Yarjejeniya
Bach ya ce, a shekarar 2014, kasar Sin ta yi nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta matasa ta birnin Nanjing, tare da bullo da sabbin wasanni a karon farko, da kuma kaddamar da dakin gwaje-gwaje na wasannin Olympics na matasa.
Tun daga wannan lokacin, hadin gwiwa tsakanin kwamitin IOC da kasar Sin ya kara karfi, bisa shirya gasar wasanni kamar gasar wasannin Olympics na lokacin hututuru ta shekarar 2022 na birnin Beijing, da gasar wasannin Asiya ta Hangzhou, da dai sauransu. Gaba daya dai, hadin gwiwar da ke tsakanin sassan biyu ya kasance cikin nasara ba tare da tangarda ba.
Ya kuma ce, a ko da yaushe, kasar Sin tana yin tsayuwar daka a kan manufar hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, kana tana goyon bayan kwamitin IOC wajen cimma kudirinsa, sannan tana kokarin tattaro ‘yan wasa daga ko ina cikin duniya domin fafatawa cikin lumana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)