Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu baya nuna wa kowane yanki bambaci, duk da damuwar da ake nuna dangane da matsalar wutar lantarki a Arewacin Nijeriya.
Yayin ziyarar da ya kai Jihar Kano, Adelabu ya bayyana cewa katsewar wutar abin takaici ne kuma ba da gangan aka yi ba.
- Za A Wallafa Makalar Shugaba Xi Don Gane Da Bunkasa Samar Da Isassun Guraben Ayyukan Yi Masu Inganci
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
Ya jaddada cewa Tinubu na girmama duk ‘yan Nijeriya kuma yana neman magance matsalar baki daya.
A lokacin ziyarar tasa, Adelabu ya bukaci gwamnatin Jihar Kano ta hada hannu da Ma’aikatar Wutar Lantarki don inganta samar da wuta mai dorewa.
Ya bayyana cewa wasu jihohi sun amfana da sabbin gyare-gyare a bangaren wutar lantarki don samar da wuta tasu ta kansu.
Ya ja hankalin Kano da ta yi amfani da irin wannan dama don samun wadatacciyar wutar lantarki.
Adelabu ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta bayar da goyon baya ga Kano domin kammala ayyukan da ke gudana don kauce wa asara.
A madadin Gwamnan Jihar Kano, Shugaban Ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, Bala Sagagi ya yaba da wannan tsari, tare da alkawarin cewa gwamnatin Kano za ta duba yiwuwar zuba jari a bangaren wutar lantarki.
Sagagi ya kuma bayyana cewa jihar na la’akari da samar da kasafin kudi don tallafa wa wutar lantarki domin rage wa al’ummar Kano biyan kudin wuta masu yawa.