Fitaccen mai hura sarewa kuma tsohon shugaban kungiyar mawakan Nijeriya (PMAN), Tee Mac Omatshola Iseli, ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su amince wajen zabin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa a zaben 2023, ya na mai cewa Tinubu bai cancanci zama shugaban kasa ba.
Tee Mac, wanda ya ce dan takarar shugaban kasan APC din surukinsa ne, ya kara da cewa, Tinubu na da shekara 86 a duniya amma yana ikirarin shi din Dan shekara 70 ne.
Ya kuma yi zargin cewa Tinubu bai da koshin lafiya kuma akwai tilin tambayoyi dangane da batun shekarunsa, tarihinsa da kuma yadda ya samu kudadensa.
Kwararren mai hura sarewar na maida martani ne kan wannan rubutun da Yemi Olakitan ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba inda ke cewa, “Kowani mutum na da damar zabin wanda yake so, amma mutum mai hankali zai tambayi kansa: wa zan zaba, shin zabin da zan yi shi ne ya dace? Mutumin ya cancanta kuwa? Mutum ne mai kima da nagarta. Ya fadi gaskiya kan shekarunsa, tarihinsa ko yadda ya samu kudi? Yana da wasaccen lafiyar da zai iya jagorantar Nijeriya a shekara 86 ko kuma zai karasa kashe kasar nan?
“Tinubu surukina ne. Matarsa Remi kannuce a gareni. Mamarta da mamata ‘yan uwan juna ne. Na san Tinubu tun 1980s har mun shirya masa zama a gidan Babana (Sir Mobolaji Bank-Anthony) a London lokacin da ya yi gudun hijira”.
A cewar Tee Mac, ya daina ziyarartar Tinubu da kai masa ziyara ne tun 2015 lokacin da ya ya kawo wa ‘yan Nijeriya Muhammadu Buhari.
“Ina tabbatar muku Tinubu bai cancanci zama shugaban kasar nan ba”.