Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya taya jigon APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar lashe zaben fitar da gwani da aka sanar a ranar Laraba.
A wata takarda da aka raba wa manema labarai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran Gwamnan, Malam Abba Anwar, Gwamnan ya danganta nasarar Asiwaju da karbuwarsa ga Arewa.
Saboda haka, Gwamnan ya gode wa masu zabe saboda hangen nesa da kaunar da suke yi wa Nijeriya da tsarin dimokuradiyya.
Har ila yau, Gwamnan ya jinjina wa shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, inda ya bayyana shi da cewa, dan halas ne mai kaunar dorewar dimokuradiyya a Nijeriya, ganin yadda ya kyale tsarin ya yi aiki babu inda-inda.
Ganduje ya bayyana Asiwaju da cewa, tamkar basilla yake wajen dinke baraka a Nijeriya, don haka ya cancanci yabo saboda jarin da ya saka na ganin dorewar dimokuradiyya.
A karshe, ya yaba wa takwarorinsa, Gwamnonin Arewa sabida jajircewa da sanin ya kamata game da juya akalar mulki zuwa shiyyar kudancin Nijeriya.