Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shirin bayar da lamuni da ake yi wa laƙabi da ‘Tertiary Institution Staff Support Fund (TISSF)’ wato Asusun Tallafawa Ma’aikatan Manyan Makarantu (TISSF) da tsabar kuɗi har naira miliyan 10, waɗanda za su gajiyar shirin sun haɗa da ma’aikatan jami’o’i da kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi da suke faɗin Nijeriya.
Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ce ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja, inda ta ce shirin zai inganta walwala da ci bunƙasa fannin ilimi.
- Gwamnati Ta Amince Da Bai Wa Jami’o’i 11 Masu Zaman Kansu Lasisi
- Hukumar Ilimin Bai Daya Za Ta Gina Dakunan Karatun Zamani A Makarantun Nijeriya
Ministan Ilimi, Dr. Maruf Alausa, ya ce wannan tallafi wani ɓangare ne na kokarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na inganta harkar ilimi a ƙarƙashin shirin *Sabunta Fata.*
Bankin Masana’antu ne zai jagoranci raba kuɗin domin tabbatar da gaskiya da bin ƙa’ida. Shugabanni daga TETFund, jami’o’i, kwalejoji da sauran masu ruwa da tsaki ne za su ci gajiyar shirin.
Ma’aikatar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tare da dukkan masu hannu da shuni don ganin an aiwatar da shirin cikin nasara da inganci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp