• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

by Bello Hamza and Sulaiman
3 weeks ago
jiragen ruwa

Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya sanar da cewa, Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya bayar da umarnin a fara aikin gyran Tashoshin Jiragen Ruwa na Apapa da Kalabar da Fatakwal da kuma ta Warri, inda aka amince da a kashe Naira biliyan daya, domin yin aikin.

 

Ya jaddada cewa, ana sa ran za a kammala aikin ne, a cikin watannin 48.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci
  • Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

Dantsoho ya bayyana haka ne, a bayan fagen taron da ake ci gaba da gudanarwa na Kungiyoyin Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa da kasa a yankin Kobe, na kasar Japan.

 

LABARAI MASU NASABA

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

Shugaban ya kara da cewa, aana sa ran aikin za a fara gudanar da shi ne, a zangon farko na shekarar 2026.

 

Ya ci gaba da cewa, aikin na yiwa wadannan Tashoshin garanbawul, na daga cikin kudurorin Gwamnatin Tarayya na zamantar da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa, musamman ta hanyar samar da kayan aiki na zamia da kuma ci gaba da janyo hankalin masu son zuba hannun jari zuwa ga fannin, wanda hakan zai kuma kara sanya gasa a cikin wadanda suke a cikin fannin.

 

Ya bayyana cewa, masu son zuba hannun jari a fannin suna ci gaba da nuna shawarsau, musamman saboda sauye-sauyen da Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinbu ta kirkiro da su, a fannin kara habaka tattalin arzkin kasar.

 

Kazalika, Shugaban ya kuma jinjinawa Ministan Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa na kan Teku Adegboyega Oyetola, musamman kan goyon bayan da yake ci gaba da bayarwa ga fannin.

 

Ya yi nuni da aiki irin wannan mai mahimmancin gaske, abu da ke bukatar isassehen lokaci domin a samu damar gudanar da ciakken shiri, duba da cewa, aiki ne, da ya kunshi bangaren injiniyoyi gudanar da bincike da sauransu.

 

Hakazalika, Dantsoho, wanda kuma shi ne, Masu Kula da Harkar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Afrika ta Yamma wato  IAPH, ya jaddda cewa, tattalin arzikin kasar nan zai kara samun dimbin masu son zuba hannun jari a fannin, musamman biyo bayan sauye-sauyen da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kirkiro da su.

 

A cewarsa, Hukumar ta NPA ta yi hadaka da sauran masu ruwa da tsaki a fanin, wanda ya sanar da cewa, hadar za ta taimaka wajen janyo ra’ayin masu son zuba hannun jari a fannin.

 

Ya yi nuni da cewa, a bayanan da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki suka bayyana a wajen taron shi ne, yadda a shekarun baya, fannin ya fuskanci rashin nuna yarda da kuma iya gudanar da shugabanci na gari, inda ya  kara da cewa, a yanzu mu muna bukatar ganin cewa, an yi hadaka domin a kara ciyar da fanning aba.

 

“Zamu yi wannan hadakar ne, ta hanyar nuna amincewa domin a cimma burin da aka sanya a gaba, na yin hadakar, “ Inji Dantsoho.

 

Shugaban ya kuma sanar da cewa, wani Kamfani da ke a kasar Singapore ya bai wa Hukumar NPA kwangila wadda za a gudanar da ita, a karkashin shirin NSW na kasar nan.

 

“Kamfanin da kayan aiki da kudade da za aiwatar da kwangilar, A cewar Shugaban.”

 

Shugaban ya kara da cewa, aikin bunkasa ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa, aiki ne da ke bukatar a kashe kudade masu yawa, wanda kuma masu zuba hannaun jari daga kasar waje ne kawai za su iya yin hakan.

 

Dantsoho ya ci gaba da cewa, duba da yadda a yau ake yin amfani da kayan aiki  na zamani dajen tafiyar da ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa a fadin duniya, dole ita ma Nijeriyata shiga cikin wannna sahun a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwa da a kasar.

 

“A yau duniya ta sauya wajen daina yin amfani da tsohon tsari wanda mutane suke gudanar da abu daya kadai,” A cewar Shugaban.

 

A cewar Shugaban Nijeriya ba ta wadatatun kudaden da za iya aiwatar da wadannan manyan ayyukan, amma muna kan ci gaba da kokarim janyo ra’ayin masu son zuba hannun jari a fannin.

 

“Akwai matukar bukatar mu yi hadaka da sauran jama’a, domin kamar yadda na bayyana a shekarar 2006, cewa ya zama wajibi Hukumar ta NPA ta daina doharo kan bangaren ggwamnati, amma ta mayar da hanjali a bangaren kamfanonin masu zaman kansu.

 

“A yanzu muna son mayar da hankali wajen zuba hannun jari ta hanyar yin amfani da fasahar zamani, kuma wannan abu ne, da ke bukatar kudade masu yawa, muna kuma kara kokari domin kulla wannan hadakar, Inji Dantsoho.

 

“A yayin da muka hallara a nan, za mu kuma kara hallara wasu taruka na da ban kuma suna yi mana kallon cewa, tabbas mu abokan yin hadaka ne,” Acewar Shugaban.

 

“Muna a cikin kungiyar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na PMAWCA, muna kuma a cikin kungiyar IAPH da kuma ta masu kula da masu tafiya cinari ta kasa da kasa wato IMO za mu kuma ci gaba da tattaunawa wadda muke da yakin za a samu sakamako mai kyau,”  Inji Dantsoho.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima
Tattalin Arziki

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026
Tattalin Arziki

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

November 7, 2025
Tattalin Arziki

Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho

November 7, 2025
Next Post
katsina

Tawagar Bankin Duniya Ta Gana Da Gwamnan Katsina Kan Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Muhallinsu

LABARAI MASU NASABA

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

November 7, 2025
An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

November 7, 2025

Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.