Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da biyan N35,000 a matsayin albashi na wucin gadi ga duk ma’aikatan gwamnatin tarayya na tsawon watanni shida, bayan tattaunawa da wakilan gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyoyin kwadagon Nijeriya NLC da TUC a ranar Lahadi.
Idan dai ba a manta ba, a taron da bangarorin biyu suka yi, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin gaggauta samar da motocin bas na dakon iskar Gas (CNG) domin saukaka matsalolin sufurin jama’a don saukakawa Jama’a kan cire tallafin man fetur.
Gwamnatin tarayya ta himmatu wajen samar da kudaden tallafi ga kananan masana’antu da rage harajin (VAT) da ke kan man dizal na tsawon watanni shida masu zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp