Amince da bayar da dukkanin lasisin da suka dace domin ci gaba da aikin hako mai a kogin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.
Karamin ministan albarkatun mai, Sanata Heineken Lokpobiri, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke kaddamar da fara gina kwalejin koyon ilimin harkokin mai da iskar gas da ke karamar hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi.
- Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai
- Wasu ‘Yan Siyasa Da Jami’an Tsaro Na Taimaka Wa Boko Haram – Zulum
Aikin hako mai da ke kogin Kolmani dai tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fara kaddamar da shi a 2022, lamarin da ke nuni da samun mai karo na farko a Arewa. Sai dai daga bisani aikin na samun jan kafa. Lamarin da ya sanya masu ruwa da tsaki da gwamnatocin Bauchi da na Gombe suka yi ta kiran da aka dawo ci gaba da aikin.
A makon jiya dai, Babban Jami’in Gudanarwar (GCEO) Kamfanin Albarkatun Mai ta kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, ya sanar da shirye-shiryen sake komawa kan ayyukan mai a kogin Kolmani da ke tsakanin Bauchi da Gombe, ya sha alwashin cewa aikin binciko mai a arewa zai ci gaba gadan-gadan.
A cewarsa, “Za mu ci gaba da hakar mai a Kolmani da sauran wurare, bayan aikin hakar mai, mun kuma himmatu wajen kammala aikin bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano.”
Ya kara da cewa wadannan ayyukan za su bayar da damar farfado da kamfanonin da suke rufe ayyukansu a baya da kuma sake ba da damar kirkiro wasu sabbi.
“Wannan ci gaban zai kyautata da kawo bukasa tattalin arzikin yankin, wanda zai daukaka kowa ta hanyar wadata kowa. Don haka dole ne mu koma wurin kuma mu ci gaba da aikin,” in ji Ojulari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp