Shugaba Bola Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da su damƙe duk wani mutum da ke nuna tutar Rasha a Nijeriya. Janar Christopher Musa, Shugaban hafsan tsaro, ne ya sanar da wannan umarni bayan taron majalisar tsaro ta ƙasa. Taron ya tattauna kan zanga-zangar da ke gudana a fadin ƙasa, wanda ya rikiɗe zuwa tarzoma a wasu jihohi.
Janar Musa ya jaddada cewa zanga-zangar, wadda ta fara cikin lumana, yanzu ta bai san a ‘yan ta’adda damar yin sace sace da tayar da hankali.
Nuna tutocin ƙetare, musamman tutar Rasha, a cikin iyakokin Nijeriya, an bayyana shi a matsayin rashin dacewa kuma a matsayin laifin cin amanar ƙasa. Shugaban ya yi gargadin cewa za a ɗauki matakin tsanani kan irin waɗannan abubuwan.
- Jami’ar Bayero Ta Dakatar Da Karatu Saboda Zanga-Zanga
- Shugaba Tinubu Ya Ɗage Zaman Majalisar Zartarwa, Ya Kira Taro Da Hafsoshin Tsaro
Shugaban hafsan tsarob ya bayyana cewa yara ne ake amfani da su don ɗaukar waɗannan tutocin, kuma an gano masu shirya wannan aiki. Ya tabbatar da cewa za a ɗauki tsauraran matakai a kan waɗannan mutane. Hukumomin tsaro sun shirya tsaf don kare dimokiradiyya da kare martabar ƙasa daga duk wani yunkuri na kawo fitina.
Shugaba Tinubu, a wani jawabi ga ƙasa da ya yi a ranar Lahadi, ya yi kira ga masu shirya zanga-zangar da su dakatar da ayyukan su tun da sun jawo tashin hankali, da asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya jaddada aniyarsa ta kare dimokiradiyya kuma ya yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri na ‘yan adawa na kawo rarrabuwar kai.