Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin gaggauta fitar da shirin samar da kiwon lafiya kyauta ga ‘yan fansho masu karamin karfi a karkashin shirin bayar da gudunmawar fansho (CPS), yana mai bayyana shirin a matsayin wani muhimmin bangare na kare mutuncin ma’aikata da suka yi ritaya.
Shugaban ya kuma yi kira da a gaggauta aiwatar da karin kudaden fansho da aka dade ana tsumayi ba tare da bata wani lokaci ba, da kuma aiwatar da mafi karancin albashi, wanda zai samar da tsaro ga mafi yawan masu karbar fansho karkashin CPS.
- “Ku Yi Murabus Idan Baza Ku Iya Rike Amanar Jama’a ba” – Gargadin Gwamna Abba Ga Kwamishinoninsa
- Jigawa Ta Fitar Da ₦1.5bn Na Lamunin Noma Ga Ma’aikatan Gwamnati Kashi Na Biyu
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba, shugaban ya bada umarnin ne bayan ya karbi bayanin Ms. Omolola Oloworaran, babbar daraktar hukumar fansho ta kasa (PenCom).
Tinubu ya kuma umurci PenCom da ta gaggauta warware matsalar fansho na ‘yansanda, yana mai jaddada cewa ‘yansandan da suka yi aiki don kare al’umma sun cancanci yin ritaya da mutunci da kwanciyar hankali.
Shugaban ya goyi bayan sauye-sauyen da aka yi, inda ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da ba da kariya ga marasa karfi na Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp