Shugaban kasa Bola Tinubu a yammacin Litinin ya dawo Abuja daga birnin Nairobi na kasar Kenya, inda ya halarci taron koli na tsakiyar shekara karo na 5 na kungiyar Tarayyar Afirka (AU).
Shugaba Tinubu ya halarci taron ne a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ECOWAS, inda ya bar Abuja a ranar Asabar.
A lokacin da yake birnin Nairobi, shugaban ya yi zama na musamman da sauran shugabannin kasashen Afirka don tantance wa da tabbatar da batutuwan da aka tattauna yayin taron jim kadan bayan kammala taron. Shugaba Tinubu ya sake nanata bukatar tabbatar da hadin kai don ci gaban kasashen yankin.
Manyan jami’an gwamnati da dama ne suka tarbi shugaban a filin jirgin saman Abuja, karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Hon. Femi Gbajabiamila; Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinnma, da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.