A yammacin ranar Talata ne shugaba Bola Tinubu ya sauka a Legas daga birnin Landan, don gudanar da bukukuwan Babbar Sallah (Eid-el-Kabir) a gobe Laraba.
Jirgin shugaban kasa Tinubu ya isa filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja, inda ya samu tarba daga dimbin magoya bayansa da ke jimirin isowarsa.
Tinubu ya shafe tsawon mako guda da barin Nijeriya inda ya halarci wani taro kan harkokin tattalin arziki a birnin Paris wanda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karbi bakunci.
Jim kadan bayan kammala taron a birnin Paris, Tinubu ya yi dan takaitaccen zango a birnin Landan na kasar Birtaniya don wata ziyara ta musamman.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp