Shugaba Bola Tinubu, a ranar Litinin, ya yi wani taro na sirri da gwamnoni shida da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba a san manufar taron ba, saboda ba a bayyana cikakkun bayanai game da maƙasudin taron ba.
Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Gwamna Umar Namadi (Jigawa), Monday Okpebholo (Edo), Biodun Oyebanji (Ekiti), Usman Ododo (Kogi), Aliyu Sokoto (Sokoto) da Nasir Idris (Kebbi).
Zaman, wanda ya dauki kusan awanni biyu, ya gudana ne a ofishin Shugaban Kasa.
Gwamnonin sun kuma ki amincewa suce uffan a lokacin da ‘yan jarida suka nemi su yi bayani bayan taron.
ADVERTISEMENT














