Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya yin jagoranci na gari wajen magance matsalar tsaro a Nijeriya.
Atiku ya faɗi haka ne lokacin da ya gana da wasu shugabannin siyasa daga Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Mohammed Kumalia.
- Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka
- Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
Ya ce ’yan bindiga da ’yan ta’adda na ci gaba da mamaye ƙauyuka tare da hana manoma yin noma, lamarin da ya kira babbar gazawar shugabanci.
Atiku ya ƙara da cewa taɓarɓarewar tsaro a yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya na nuna cewa gwamnati ba ta yi abin da ya dace don kare rayukan jama’a ba.
Ya jaddada cewa dakarun tsaron Nijeriya suna da ƙarfin da za su iya fatattakar ’yan ta’adda, amma abin da ya rage shi ne samun ingantaccen shugabanci da ƙwarin gwiwa daga fadar shugaban ƙasa.
Atiku ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai domin ceto ƙasar nan, inda ya bayyana cewa dawo da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziƙi ya kamata su zama fifiko.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp