Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis ya hadu tare da sauran shugabannin kasashen duniya a Paris-France a wajen babban taron kan yarjejeniyar kwaskwarima ga tsarin hada-hadar kudi na duniya, wacce kai tsaye hakan zai taimaka wajen rage kaifin talauci, shawo kan basuka ko sokewa da kuma la’akari da kananun kasashen da annobar Korona ta raunata.
Tinubu ya halarci wurin taron da ke Palais Brongniart, da karfe 8.59 am agogon Nijeriya domin halartar bude taron sabon tsarin hada-hadar kudi na duniya, inda ya samu tarba daga ministan Faransa da ke kula da harkokin kasashen waje, Catherine Colonna.
A sanarwar manema labarai, Dele Alake, da yake marabtar bakin, shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce, babban taron na da manufar hada tunani waje guda ne domin samar da sabon tsarin hada-hadar kudi na duniya wanda hakan zai taimaka sosai wa kasashe masu tasowa wajen sauyin makamashi, yaki da talauci da fatara, tare da muunta ‘yancin kowace qasa domin kyautata rayuwa.
Shugaban na Faransa, ya kara cewa kasashen Afrika suna kan gaba wajen fuskantar manyan matsaloli, tare da tulin basuka da suke janyo koma baya ga cigaban kasashen, don haka ya ce, taron zai taimaka wajen fuskantar irin wadannan matsalolin domin neman mafiya.
“Annobar Korona ta janyo wahala da mawuyacin yanayi matuka, yanzu muna fuskatar yakin Ukraine da ya janyo babban matsala ga tattalin arziki,” ya shaida.
Macron ya shaida wa shugabannin kasashen 50, akwai bukatar sake zurfin nazari wajen ganin yadda za a tafiyar da kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyi domin ganin kowani bangare na amfanuwa da juna tare da maida hankali kan masu rauni don a tafi tare.
Ya ce, babban matsalar fatara da talauci tabbas na bukatar hada karfi da karfe tare da fito da muhimman dabaru da hikomin shawo kansa, “Ya kamata dukkaninmu mu yarda cewa babu wata kasa da za ta iya magance matsalar fatara ita kadai,” ya kara.
Macron ya ce, tsarin da za a fitar din zai hada da masu ruwa da tsari a kasashen, shiyoyi, shigo da kamfanoni da cibiyoyi masu zaman kasnu musamman irin International Monetary Fund da bankin duniya World Bank domin fito da matakan kawo gyara.
Ya sake nanata cewa kamfanoni masu zaman kansu na da gayar muhimmanci a janyo su jika wajen fitar da sabon tsari domin fuskantar cigaba mai ma’ana, kazalika, ya ce, a irin lokacin da ake neman kawo sauyi ga sashin hada-hadar kudade akwai wasu fannonin da suke bukatar kula da suka hada da kiwon lafiya, ilimi da wadatar abinci.
A madadin kasashen Afrika kuwa, shugaban jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum, ya ce, dole sabon yarjejeniyar ya kasance cikin hanzari da muhimmanci ga Afrika sannan, tsarin da za a fitar din a yi wajen tsage gaskiya domin tabbatar da a zahirance kasashe masu tasowa sun amfana a matsayin abokan jere.
Bazoum ya ce, matsalolin talauci da kwararowar hamada sun addabi kasashensu, da ke shafar zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar.
A cewarsa, “A Afirka muna bukatar taimako wajen shimfida ayyuka, kiwon lafiya, wadatar abinci da ilimi.”
Sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ya shaida wa shugabannin cewa taron na da bukatar yin tsarin da kowa zai ji a jikinsa ya dace a aiwatar ba wai a zana a watse ba kawai.
Guterres ya ce, kasashe da dama har yanzu suna fama da radadin illar da annobar Korona ta musu da kuma na dumamar yanayi, da yakin Ukraine da dai sauransu.
Guterres ya kara da cewa, kasashen Afirka ba su samu wadataccen hanyoyin biyan basukan da suke makale a wuyayensu, da hakan ke barazanar cewa nan gaba al’ummar da ke tasowa za su iya shiga mawuyacin hali sakamakon wannan tulin basukan.
Ya ce, tsarin yarjejeniyar kudin na da bukatar ya duba wadannan matsalolin ta yadda za a shigar cikin tsarin domin shawo kan tulin matsalolin da suke akwai, ya nuna damuwarsa kan basukan da ke kan kasashen Afrika, inda ya nuna hasken cewa ta hanyar kyakkyawar tsarin da aiki tukuru za a iya magance wasu daga cikin matsalolin.
Sakataren ya nuna bukatar da ke akwai ga shugabannin duniya da su hada hannu wajen fuskantar matsalolin da suke akwai domin samar da mafita da cigaban kasashe masamman masu tasowa.
Wani masani kan dumamar yanayi, Vanessa Nakate, da ya fito daga kasar Uganda, ya yi nemi a dan yi shiru domin jinjina wa marasa galihu da wadanda suke cikin mawuyacin hali a duniya, yana mai cewa karya al’kawura idan aka dauka na gurguntar da rayuwar mutane da dama a kasashe masu tasowa.
Tunin shugabannin da jagororin manyan kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyi suka tsunduma cikin taron domin nema hanyoyin da za a fitar da tsarin yarjejeniya da ake kyautata zaton zai taimaka sosai wajen rage talauci da basuka a kasashen duniya.