A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban kasa, Bola Tinubu, ya isa birnin New York domin halartar manyan tarukan babban taron majalisar dinkin duniya karo na 78.
Tinubu ya isa filin jirgin sama na JF Kennedy da ke birnin New York da misalin karfe 6:45 na yamma agogon kasar.
- lKungiyar Kwadago (NLC) Na Shirin Tunduma Wani Sabon Yajin Aiki Mai Dogon Zango
- Tinubu Ya Nada Jamila Da Olawande A Matsayin Ministocin Matasa
Shugaban kasar dai yana jagorantar tawagar Nijeriya ne domin halartar taron da aka shirya gudanarwa tsakanin ranakun 18 zuwa 26 ga watan Satumba, wanda shi ne karon farko da zai fara aiki a matsayinsa na shugaban kasar Nijeriya.
Shugaban ya samu tarba daga ministan harkokin wajen kasar Amb. Yusuf Tuggar, wakilin dindindin na Nijeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Amb.Tijjani Muhammad-Bande, da Maj.-Gen. Dangana Allu.
A wannan karon jami’ai uku ne kadai suka kasance a filin jirgin domin tarbar shugaban tare da sauran jami’an Nijeriya da ke a otel din UN Plaza Millenium Hilton domin tarbarsa.
Tinubu, a jawabinsa da zai gabatar a majalisar, zai yi jawabi ga shugabannin duniya da yammacin ranar Talata da misalin karfe 6 na yamma agogon kasar.
Shugaban Nijeriyar zai kasance shugaban Afrika na biyar da zai yi jawabi a rana daya daga cikin ranakun taron kuma mai magana na 14 daga cikin shugabannin 20 da aka shirya yin jawabi a ranar Talata.
Jawabin na Tinubu zai ƙunshi batutuwa da dama da suka hada da ci gaba mai dorewa, sauyin yanayi, haɗin gwiwar duniya, da kuma mahimmancin magance rashin daidaito da rikice-rikicen jin kai na duniya.
A ranar Laraba ne ake sa ran shugaban Najeriya zai shiga cikin babban taron tattaunawa kan samar da kudade don samar da ci gaba.
Zai halarci wani babban taro kan rigakafin cutuka da bayar da amsoshin wasu tambayoyi da za a bijiro masa.