Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Rome, Italiya, domin halartar taron shugabannin ƙasashe na Aqaba, wanda zai mayar da hankali kan matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a Yammacin Afrika. Jirgin Shugaban ƙasar ya sauka a filin jirgin saman Rome Fiumicino da misalin ƙarfe 7:20 na yamma a ranar Lahadi.
Taron, wanda Jordan da gwamnatin Italiya ke jagorantarsa tare, zai fara ne a ranar Talata. Ana sa ran shugabannin ƙasashe, da jami’an leƙen asiri, da hafsoshin Soji, da wakilan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da na agaji za su halarta.
- Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Maryam Sanda Afuwa Bayan Shafe Shekaru 6 A Gidan Yari
- Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC
Taron Aqaba, wanda Sarki Abdullah II na Jordan ya kafa a shekarar 2015, na nufin ƙarfafa haɗin kai a yaƙi da ta’addanci a duniya. Bana, taron zai mayar da hankali ne kan barazanar da ke fitowa daga yaɗuwar ƙungiyoyin ta’addanci, da haɗin kai tsakanin laifuka da ta’addanci, da kuma haɗarin da ke tasowa daga ƴan tawaye na Sahel zuwa teku a yankin Gulf.
Masu halarta za su tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen yanki, katse hanyoyin sadarwar dijital da ake amfani da su wajen yaɗa akida ko jan sabbin mabiya, da kuma daƙile yaɗuwar tsattsauran ra’ayi ta kafafen intanet.
Mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Tinubu zai yi wasu muhimman ganawa da shugabannin ƙasashe a gefen taron don ƙarfafa haɗin kai a fannin tsaro da kwanciyar hankali na yanki.