Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya isa Jihar Legas a ranar Laraba don gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Ya isa Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed, inda Gwamna Babajide Sanwo-Olu da wasu jami’an gwamnati suka tarbe shi.
- Taron Beijing: Magance Korafe-korafen Al’umma Na Karfafa Shugabanci A Matakin Farko
- Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Tarayya Za Ta Tsawaita Kasafin 2024 Zuwa Watanni 6 – Akpabio
Tun da farko, Tinubu ya gabatar da kasafin kudi na Naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025 mai taken “Kasafin Daidaito” ga Majalisar Dokokin Kasa.
Kasafin kudin ya ce zai mayar da hankali kan tsaro, gina ababen more rayuwa, ilimi, da kiwon lafiya.
An ware Naira tiriliyan 4.91 ga tsaro, Naira tiriliyan 4.06 ga ababen more rayuwa, Naira tiriliyan 3.5 ga ilimi, da kum Naira tiriliyan 2.4 ga kiwon lafiya.
Shugaban ya bukaci ‘yan Nijeriya su hada kai don magance kalubalen kasa.