Shugaban kasa, Bola Tinubu ya dawo babban birnin tarayya Abuja a yammacin Lahadin nan daga Legas, kwanaki 13 bayan tafiyarsa don halartar taron koli kan sabuwar yarjejeniyar hada-hadar kudade ta duniya da aka yi a birnin Paris na kasar Faransa.
Shugaban ya koma Legas ne a ranar Talatar da ta gabata a daidai lokacin da ake gudanar da bikin babbar sallah.
- Dole Ne Mace Ta Gaya Wa Mijinta Gaskiya Domin Ranar Hisabi – Matar Gwamnan Jigawa
- Saudiyya Ta Tsare Mutum 17,000 Da Suka Yi Yunkurin Hajji Ba Tare Da Izini Ba
Idan za a tuna cewa a lokacin da ya bar Abuja, Shugaba Tinubu ya halarci sabuwar yarjejeniya ta hada-hadar kudade ta duniya a birnin Paris.
Ya bar birnin Paris zuwa birnin Landan na Birtaniya a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni, a wata ziyarar sirri.
Ya gana da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a birnin Landan.
Yayin da ya ke Legas, baya ga haduwa da wasu ‘yan Nijeriya domin gudanar da bikin babbar sallah, ya kuma tarbi shugaban kasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo, a ranar Asabar.