Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Baffa Dan Agundi a matsayin sabon Darakta-Janar na cibiyar inganta aikin ta ƙasa. Baffa Dan Agundi ya taɓa yin aiki a matsayin shugaban masu rinjaye na Majalisar Dokoki ta Jihar Kano da kuma Babban Sakataren Kotun Manyan Laifuka ta Jihar Kano.
A cewar Ajuri Ngelale mai ba shugaba Tinubu sawara kan harkokin yada labarai, Shugaba Tinubu yana sa ran Baffa Dan Agundi zai nuna cikakken sadaukarwa da kishin ƙasa wajen inganta ayyukan cibiyar.
- Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci
- Tinubu Ya Nada Abubakar Dantosho Manajan NPA
Wannan yana nufin samar da al’adar ingantaccen aiki da kuma ƙarfafa tunanin aiki don samun kyakkyawan sakamako da inganta rayuwa a Nijeriya.
Wasu daga cikin mukaman da Baffa Dan Agundi ya riƙe sun haɗa da; shugabancin hukumar KAROTA da hukumar haƙƙin masu sayayya ta Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp