Shugaba Bola Tinubu ya nada Dakta Abubakar Dantsoho a matsayin Manajan Darakta na Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA).Â
Dokta Dantsoho ya yi digiri na uku a fasahar teku daga Jami’ar Liverpool John Moores da kuma digiri na biyu a harkar sufuri daga Jami’ar Cardiff.
- Kafa Masana’antun Sarrafa Ridi Da Sauyin Da Ake Samu A Jihar Yobe
- Matasa Za Su Amfana Da Shirin Noma Don Samun Riba
Ya gudanar da ayyuka daban-daban a NPA, ciki har da Mataimakin Babban Manaja a hukumar.
Talla
Tinubu ya nada Sanata Adedayo Adeyeye a matsayin shugaban hukumar NPA.
Adeyeye wanda tsohon Ministan Ayyuka ne kuma tsohon Sanata na Ekiti ta Kudu.
Shugaba Tinubu yana tsammanin sabon jagoranci zai inganta ayyukan tashar jiragen ruwa da inganta sakamako a hukumar.
Talla