Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da nadin Ajuri Ngelale a matsayin babban mashawarcin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a kuma mai magana da yawunsa.
Kamar yadda wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta nakalto a ranar Litinin da yammaci, nadin na Ajuri ya fara aiki ne nan take daga ranar 31 ga watan Yulin 2023 kuma zai kare ne zuwa karshen gwamnatin Tinubu in dai ba wata matsaya shugaban ya sake dauka ba.
Tinubu ya bukaci sabon mai magana da yawunsa da ya yi amfani da kwarewa da gogewarsa wajen gudanar da aikin da ke gabansa a halin yanzu.
Da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan wannan nadin, Ngelale ya ce, ya yi matukar farin ciki da annashuwa bisa zabin da shugaban ya masa, tare da shan alwashin zai yi aiki tukuru domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Ya ce, jawo wasu karin hannaye wajen haduwa a yi aiki tare wani gagarumin abun yabo ne kuma zabinsa a matsayin kakaki dama ce a gareshi da zai yi aiki da kyau.
“A kodayaushe zan kasance mai yin aiki da himma da kwazo. Ina kaunarku dukka,” Ngelale ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan sanar da nadinsa da gwamnatin ta yi.