Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabbin mambobin hukumar gudanarwa alhazai ta kasa (NAHCON).
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a yammacin ranar Laraba, shugaban kasar, a kudurinsa na ganin an gudanar da ayyukan Hajji na shekarar 2024, ba tare da wata matsala ba, ya nada Jalal Arabi a matsayin shugaban hukumar gudanarwar hukumar.
- Hajjin Badi: Dalilin Kara Kudin Kujera Zuwa Naira Miliyan 4.5 – NAHCON
- Harin Boko Haram Ya Yi Ajalin Mutane 7 A Yobe
LEADERSHIP ta ruwaito cewa ‘yan makonnin da suka gabata ne shugaba Tinubu ya nada Arabi a matsayin shugaban riko na hukumar NAHCON.
Sabbin mambobin hukumar gudanarwar sun hada da Aliu Abdulrazaq, Prince Anofi Elegushi da Farfesa Abubakar A. Yagawal
Sauran mambobin su ne Muhammad Umaru Ndagi, Abba Jato Kala, Sheikh Muhammad Bin Othman, Tajudeen Oladejo Abefe, Aishat Obi Ahmed, Zainab Musa, Farfesa Musa Inuwa Fodio — Jama’atul Nasril Islam (JNI), da Farfesa Adedimizi Mahfouz Adebola — Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (SCIA).
Ngelale ya kara da cewa, shugaban kasar ya umurci wadanda aka nada da su sadaukar da kansu wajen ganin cewa ayyukan hukumar alhazai ta kasa sun kasance masu inganci da gaskiya da kuma biyan bukatun ‘yan Nijeriya.