Shugaban Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin kwamishinonin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da za su yi aiki a matsayin kwamishinonin hukumar a jihohi, su tara da kowannen su ke da damar rike mukanin na tsawon shekara biyar, inda suke tsumayin tabbatar da su daga majalisar dattawan Nijeriya.
A wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya ce an yi nadin ne bisa dogara da sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulkin kasa ta 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) da sashe na 6 na dokar zabe ta 2022 da suka bai wa shugaban kasar cikakken ikon nadin.
- UNESCO Ta Yi Bikin Ranar Amfani Da Kafofin Watsa Labarai Da Yada Bayanai Ta Duniya A Abuja
- Kasuwanci Tsakanin Sin Da Zimbabwe Ya Bunkasa
Wadanda aka nadan su ne:
Isah Shaka Ehimeakne — Kwamishinan zabe (REC) a jihar Edo
Bamidele Agbede — Kwamishinan zabe (REC) a jihar Ekiti
Jani Adamu Bello — Kwamishinan zabe (REC) a jihar Gombe
Taiye Ilayasu — Kwamishinan zabe (REC) a jihar Kwara
Bunmi Omoseyindemi — Kwamishinan zabe (REC) a jihar Lagos
Yahaya Bello — Kwamishinan zabe (REC) a jihar Nasarawa
Mohammed Yalwa — Kwamishinan zabe (REC) a jihar Neja
Anugbum Onuoha — Kwamishinan zabe (REC) a jihar Ribas
Abubakar Fawa Dambo — Kwamishinan zabe (REC) a jihar Zamfara
Ngelale, ya ce shugaban kasa na sa ran sabbin wadanda aka nada za su kasance masu nuna kwarewa da bin ka’idoji da dokoki yayin gudanar da ayyukan da ke gabansu hadi da tabbatar da gaskiya gogewa da kwarewa domin tabbatar da zabe mai inganci kuma sahihi a kasar nan.