Shugaba Bola Tinubu ya nada Musa Adamu Aliyu a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC).
Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya tabbatar da nadin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da ‘Ya’Ya 2 Na Dan Majalisar Dokokin Jihar Kwara
- Zulum Ya Soke Lasisin Hanyar Layin Dogo Da Aka Yi Watsi Da Shi
Shugaban ya kuma amince da Clifford Okwudiri Oparaodu a matsayin sakataren hukumar.
Sanarwar ta ce, “An zabi sabon Shugaban Hukumar ICPC ne domin tabbatar da shi.”
Majalisar dattawa, ta biyo bayan amincewar shugaban kasa na bukatar shugaban mai barin gado na ci gaba da hutun kafin karshen wa’adinsa daga ranar 4 ga Nuwamba, 2023, gabanin ranar 3 ga Fabrairu, 2024.
“Matsayin Sakataren Hukumar ba ya bukatar amincewar Majalisar Dattawa, saboda haka, bisa umarnin Shugaban kasa, nadin Mista Clifford Okwudiri Oparaodu a matsayin Sakataren Hukumar ya fara aiki nan take.
“Dakta Musa Adamu Aliyu ya fara yin gyare-gyare da dama a matsayin babban Lauyan Jihar Jigawa tun daga watan Satumban 2019 kuma yana da digiri na biyu a fannin Shari’a. An kuma nada shi a matsayin Babban Lauyan Nijeriya (SAN) a watan Oktoba 2023.
“Clifford Okwudiri Oparaodu lauya ne wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana aiki kuma ya yi aikin gwamnati a matsayin mamba a hukumar shari’a ta jihar Ribas kuma shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Fatakwal.
“Shugaban ya bukaci sabbin shugabannin hukumar ICPC da su kasance a kan gaba yayin da suke gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ko nuna son zuciya ba dangane da duk wani abu da ke gabansu.”