Shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi majalisar wakilai ta amince da neman bashin Naira tiriliyan 1.15 domin cike giɓi a kasafin kuɗin shekarar 2025.
A cikin wata wasiƙa da mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, ya karanta, Tinubu ya bayyana cewa ƙarin da aka yi wa kasafin kuɗi ya samar da giɓi sama da abin da aka amince da shi a baya wajen samun kuɗin shiga da rance.
- Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
- Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
Ya ce za a karɓo bashin ne daga cikin gida don cike giɓin, bisa tanadin dokar Fiscal Responsibility Act.
Kasafin kuɗin 2025 ya ƙaru daga Naira tiriliyan 49.74 zuwa tiriliyan 59.99, wanda ya haifar da giɓin Naira tiriliyan 14.1, yayin da aka amince da rance na tiriliyan 12.95 kawai.
Majalisar ta tura buƙatar shugaban ƙasa zuwa kwamitin tallafi, rance da kula da bashi domin yin nazari da bayar da rahoto ga majalisar don ɗaukar mataki na gaba.














