Shugaba Bola Tinubu ya aike da takardar neman amincewar majalisar wakilai, kan karɓo lamunin dala biliyan $2.347 daga ƙasashen ƙetare.
Wannan ya ƙunshi sabon lamunin ƙetare na Naira Tiriliyan 1.843, a kasafin kudi, kan canjin dala $1.00/N1,500.00) a cikin kasafin kuɗi na shekarar 2025 don cike giɓin kasafin kuɗin.
Takardar ta bayyana cewa, za a karɓo lamunin ne ta ɗaya daga cikin waɗannan zaɓukan da ke cikin Babbar Kasuwar Duniya (ICM).
Tinubu, a cikin wata wasika da ya aikewa kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen wanda ya karanta a zaman majalisar a ranar Talata, ya kuma buƙaci majalisar ta amince da batun shirin Sukuk da zai kai kusan dala miliyan $500 a cikin ICM.