A ranar Talata, shugaba Bola Tinubu, ya nemi amincewar majalisar dattawa domin tabbatar da sabbin shugabannin Hafsoshin tsaro da ya nada.
Bukatar Tinubu na kunshe ne a cikin wata wasika da aka aika wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kuma aka karanta a zauren majalisar.
- Tinubu Ya Yi Ganawarsa Ta Farko Da Hafsoshin Tsaro
- Da Dumi-Duminsa: Tinubu Ya Kori Hafsoshin Tsaron Nijeriya, Ya Nada Sabbi
Tinubu a cikin wasikar ya ce:
“A bisa tanadin sashe na 18 karamin sashe na 1 na dokar Sojoji ta shekarar 2004, ina me gabatarwa majalisar dattawa wadanda aka nada a matsayin Hafsan Hafsoshin Soji da Hafsoshin Soja na kasa domin tantancewa,l.
“Babban Hafsan Sojoji, Maj. Gen. C.G Musa, Shugaban Hafsan Sojoji, Maj. T. A Lagbaja, Hafsan Sojan Ruwa, Rear Admiral Emmanuel Ogalla, Shugaban Hafsan Sojan Sama, AVM H.B Abubakar.
“Muna bukatar Majalisar Dattawa da ta lura da yanayin tsaron da kasarmu ke ciki a halin yanzu, wanda ke bukatar hadin kai tsakanin ‘yan majalisa da na zartaswa don tabbatar da tsaro mai inganci.
“Wannan ya hada da sake duba da nazarin yadda tsare-tsaren yanayin tsaronmu da nadin sabbin shugabanni don yin aiki tare da juna don cimma matakin da ake sa ran samu.
“Ina fatan bukatar za ta sami karbuwa da tabbatarwa daga Majalisar Dattawan Nijeriya, ” in ji Tinubu.