Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da mai Shari’a Kudirat Olatokunbo Kekere-Ekun a matsayin babbar Alƙalin Nijeriya na 23 a yau Litinin, inda ta zama mace ta biyu da ta riƙe wannan matsayi a tarihin Nijeriya.
A lokacin bikin rantsuwar da aka gudanar a fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, Tinubu ya sake jaddada jajircewar gwamnatinsa kan ƴancin ɓangaren shari’a, yana mai bayyana muhimmancinsa wajen kiyaye tsarin mulkin dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Ya yi nuni da cewa dole ne a tabbatar da cewa shari’a ta kasance ginshiƙin da ba za a taɓa tsoma baki ba, domin kare haƙƙin al’umma da tabbatar da adalci.
Shugaban ƙasar ya yaba da nasarar da mai Shari’a Kekere-Ekun ta samu a wannan fanni mai cike da maza, yana mai bayyana ta a matsayin abin koyi ga matan Nijeriya.
Bikin ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da tsohon babban Alƙalin Nijeriya, da Shugaban majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, da kuma iyalan sabuwar mai Shari’a Kekere-Ekun.