• English
  • Business News
Sunday, July 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Dokar Rage Farashin Mai Da Iskar Gas

by Abubakar Sulaiman
1 month ago
in Manyan Labarai
0
Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Dokar Rage Farashin Mai Da Iskar Gas
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan wata sabuwar doka ta musamman da za ta rage farashin haƙo mai da iskar gas a Nijeriya. Wannan mataki na da nufin jawo sabbin masu zuba jari da kuma ƙara kuɗaɗen shiga na gwamnati.

Dokar da ake kira ‘Dokar Taimako Don Rage Farashin Ayyukan Mai Da Iskar Gas, 2025’ za ta ba da gudummawar haraji ga kamfanonin mai da gas da suka rage farashin ayyukansu bisa ƙa’idojin masana’antu. Kamfanonin da suka cimma waɗannan mataki za su iya samun kashi 50% na ƙarin kuɗin da gwamnati za ta samu daga rage farashin.

  • Za Mu Ci Gaba Da Aikin Neman Man Fetur Arewacin Nijeriya — Ojulari
  • Tsadar Farashin Ƙwai Ya Sa Ƴan Nijeriya Sun Haƙura Da Cinsa

Duk da haka, gudummawar harajin ba za ta wuce kashi 20% na harajin da kamfani ke biya a shekara ba, domin tabbatar da daidaito tsakanin taimakon masu zuba jari da kuma kula da kuɗin shigar gwamnati.

Shugaba Tinubu ya ce, “Wannan doka ta nuna cewa mun himmatu wajen gina masana’antar mai da gas mai inganci, da zata yi takara da juna (competition), don amfanin ’yan Nijeriya. Yana da muhimmanci ga makomar ƙasa, samar da ayyukan yi, da kuma amfani da kowace gangar mai.”

Hukumar kula da mai da Iskar Gas ta Nijeriya (NUPRC) za ta fitar da ƙa’idodin farashi na shekara-shekara don ayyuka daban-daban kamar a ƙasa, da ruwa mai zurfi, da tekun zurfi. Za a kuma fitar da cikakkun bayanai game da wannan dokar a cikin ’yan makonnin nan. Gwamnati ta yi imanin cewa wannan dokar za ta ƙara inganci a fannin mai da iskar gas.

Labarai Masu Nasaba

2027: Shugabannin Hamayya Sun Bazama Neman Goyon Baya A Yankunansu

Shettima Ya Ziyarci Buhari A Landan Cikin Sirri Don Duba Lafiyarsa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: FeturGasOilTinubu
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 60 A Borno

Next Post

Han Zheng Ya Halarci Bikin Bude Tattaunawa Ta Hudu Kan Musaya Da Koyi Da Juna A Tsakanin Al’ummomi Ta Fannin Wayewar Kansu

Related

2027: Shugabannin Hamayya Sun Bazama Neman Goyon Baya A Yankunansu
Manyan Labarai

2027: Shugabannin Hamayya Sun Bazama Neman Goyon Baya A Yankunansu

19 hours ago
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna
Labarai

Shettima Ya Ziyarci Buhari A Landan Cikin Sirri Don Duba Lafiyarsa

19 hours ago
Sojoji Sun Cafke Wani Soja Kan Mutuwar Mai Gyaran Waya A Adamawa
Kotu Da Ɗansanda

Sojoji Sun Cafke Wani Soja Kan Mutuwar Mai Gyaran Waya A Adamawa

22 hours ago
Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
Manyan Labarai

Lauyoyin Natasha Sun Buƙaci Ta Koma Majalisa Ranar Talata Bayan Miƙa Takardun Hukuncin Kotu

22 hours ago
Sojoji Sun Sake Ceto ‘Yan Matan Makarantar Chibok 2
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Mutum 2 Da AK-47 A Taraba

2 days ago
Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista
Manyan Labarai

Shugabannin Jam’iyyar ADC Na Jihohi 36 Da Abuja Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga David Mark

2 days ago
Next Post
Han Zheng Ya Halarci Bikin Bude Tattaunawa Ta Hudu Kan Musaya Da Koyi Da Juna A Tsakanin Al’ummomi Ta Fannin Wayewar Kansu

Han Zheng Ya Halarci Bikin Bude Tattaunawa Ta Hudu Kan Musaya Da Koyi Da Juna A Tsakanin Al'ummomi Ta Fannin Wayewar Kansu

LABARAI MASU NASABA

Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Peter Rufai, Fitaccen Golan Nijeriya

Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Peter Rufai, Fitaccen Golan Nijeriya

July 13, 2025
Dan Gidan Ancelloti Ya Zama Sabon Kocin Botafago FC

Dan Gidan Ancelloti Ya Zama Sabon Kocin Botafago FC

July 13, 2025
NAFDAC Da Masu Maganin Gargajiya Za Su Tsabtace Sana’ar Sayar Da Maganin Gargajiya A Nijeriya

NAFDAC Da Masu Maganin Gargajiya Za Su Tsabtace Sana’ar Sayar Da Maganin Gargajiya A Nijeriya

July 12, 2025
Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

July 12, 2025
Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

July 12, 2025
Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

July 12, 2025
Yadda Iyaye Ke Rungumar Bokaye Don Samar Wa ‘Ya’yansu Mata Mazaje Masu Kudi

Yadda Iyaye Ke Rungumar Bokaye Don Samar Wa ‘Ya’yansu Mata Mazaje Masu Kudi

July 12, 2025
Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani

Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani

July 12, 2025
Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

July 12, 2025
Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya

Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya

July 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.