Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2025 na Naira tiriliyan 54.99 a fadar gwamnati dake Abuja a ranar Juma’a. Majalisar Dokoki ta ƙasa ta amince da kasafin ne a ranar 13 ga Fabrairu bayan ta ƙara adadin daga Naira tiriliyan 49.7 da aka gabatar tun farko.
Kasafin ya ƙunshi Naira tiriliyan 3.65 domin sauya-sauyen doka, Naira tiriliyan 13.64 na kuɗaɗen tafiyar da gwamnati, Naira tiriliyan 23.96 don ayyukan raya ƙasa, da Naira tiriliyan 14.32 domin biyan basussuka. Giɓin kasafin kuɗin na 2025 ana hasashen zai kasance kashi 1.52% na GDP.
- Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Amince Da Tiriliyan 54.9 Kasafin Kuɗin 2025
- Sojojin Nijeriya Za Su Fara Karɓar N3,000 Kudin Abinci A Rana
Wannan kasafi shi ne mafi girma a tarihin Najeriya, domin ya ninka na shekarar 2024 wanda ya tsaya kan Naira tiriliyan 27.5. Ƙarin kuɗin ya danganta ne da yunƙurin gwamnati na zuba jari a manyan ayyuka da rage gibin tattalin arziki.
Ana sa ran ƙarin bayani kan yadda za a aiwatar da kasafin kuɗin da tasirinsa kan bangarorin tattalin arziƙi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp