Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, wanda ya ziyarci Jihar Benuwai tare da shugaban kwamitin leken asiri da tsaro na majalisar dattawa, Uba Umar, ya bayyana hare-haren da kashe-kashen a matsayin mummunan aiki.
”Abin da ya faru bala’i ne kuma mummunan aiki. Masifa ne ya ziyarci jihar. Amma idan mugunta ta zo, dole ne mutanen kirki su hada kai don fuskantar ta,” in ji shi.
- Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira A Ranar Juma’a A Maiduguri
- Shenzhou-20: Kasar Sin Ta Aike Da ‘Yan Sama Jannati 3 Zuwa Sararin Samaniya
NSA ya kara da cewa, “Shugaban kasa yana tare da ku. Wannan lokaci ne mai wahala a gare da kuma mu duka.
”Wannan lokaci ne na bakin ciki, kuma a cikin irin wadannan lokutan ne kuka san wadanda ke kulawa da ku da gaske.”
Ribadu ya bayyana cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta gaji tashin hankali da ke fama da shi a kasar nan, kuma tana aiki tukuru don gyara abubuwan da suka lalace.
Ya ce, “Na zo nan ne don in jajanta muku da sauran mutanen kirki na Benuwai kan asarar rayuka da aka yi da kuma tabbatar muku da cewa muna tare da ku.
“Benuwai jiha ce mai matukar muhimmanci a Nijeriya. Ta kasance daya daga cikin jihar da ake samar da abinci a kasa, ita ce ta farko wurin samar da abinci, kuma muna alfahari da hakan.
“Za mu magance wannan matsalar. Ka ku kadai ku ce jin zafin ba, wannan kalubalen ya shafi mu duka. Lokacin da ibtila’i ta zo, mutanen kirki dole ne su hadu don fuskantar ta.
“Sojojinmu da hukumomin tsaro suna yin iya bakin kokarinsu, amma irin wannan lamarin yana ci gaba da faruwa ne saboda ba zai yiwu a tura jami’an tsaro zuwa kowane kauye ba.
“Kasashe suna fuskantar mawuyacin hali. Rashin tsaro kalubale ne mai wuyan shawowa.
“Haifar da tashin hankali abu ne mai sauki, amma warware matsalolin da ke tattare da su ya fi wahala, duk da haka muna yin iya bakin kokarinmu.
“A matsayinmu na gwamnatin da ba ta cika shekaru biyu ba, mun riga mun rage yawan tashin hankalin da muka gada.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp