Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Tsohon shugaban Nijeriya ya rasu a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a birnin Landan bayan fama da doguwar rashin lafiya.
- Tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari Ya Rasu A Landan
- Shettima Ya Ziyarci Buhari A Landan Cikin Sirri Don Duba Lafiyarsa
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya tattauna da uwargidar marigayin, Hajiya Aisha Buhari, inda ya miƙa ta’aziyya da alhini kan wannan babban rashi.
Shugaba Tinubu ya umarci mataimakinsa, Kashim Shettima, da ya tafi zuwa birnin Landan domin dawo da gawar marigayin zuwa gida Nijeriya.
Buhari ya ci zaɓen shugaban ƙasa har sau biyu — a 2015 da 2019. Haka kuma, ya shugabanci ƙasar a matsayin shugaban mulkin soja daga Janairu 1984 zuwa Agusta 1985.
Shugaba Tinubu ya bayar da umarni a sauke tutocin Nijeriya zuwa rabin sanda a matsayin girmamawa ga marigayi shugaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp