Shugaba Bola Tinubu ya taya fitattun yan Nijeriya biyu, Farouk Gumel da Tobi Amusan murnar samun nasarori a bangarori daban-daban, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata ta hannun mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, shugaban Nijeriyar ya bayyana nasarorin da suka samu a matsayin abin alfaharin kasa.
A kwanakin baya ne aka nada Gumel a matsayin shugaban gidauniyar Botswana Sovereign Wealth Fund Limited, matsayin da shugaban kasar ya ce ya nuna kwazonsa da kuma daukakar kwararrun yan Nijeriya a kasashen duniya, shugaban ya yaba da irin nasarorin da Gumel ya samu, musamman a matsayinsa na mataimakin shugaban Afrika a kungiyar masu zuba jari ta Tropical General Investment Group, inda ya bayar da gudunmawa sosai wajen samar da wadataccen abinci a Nijeriya.
Jagorancinsa ya zama abin alfahari ga al’ummarmu, kuma ina da yakinin zai yi fice tare da kara tabbatar da martabar Nijeriya a fannin kudi a duniya,” in ji Tinubu, haka kuma shugaban kasar ya yabawa yar wasan tsalle-tsalle ta Nijeriya Tobi Amusan, wacce ta samu lambar azurfa a gasar tseren mita 100 na mata a ranar Litinin a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya na shekarar 2025 da ake gudanarwa a birnin Tokyo na kasar Japan.
Shugaban ya yaba da abinda ya kira kwarewa da juriya irin na Amusan, tare da cewa aikinta ya sake misalta irin daukakar da yan Nijeriya za su iya samu ta hanyar aiki tukuru da nuna kwazo, Tinubu ya yi fatan Gumel da Amusan su ci gaba da samun nasara a ayyukansu tare da ba su tabbacin gwamnati za ta ba su cikakken goyon baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp