Shugaba Bola Tinubu ya taya shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, murnar lashe zaben da ya sake yi.
Tinubu, wanda ya yi amfani da shafinsa na Twitter a karon farko a matsayin shugaban Nijeriya a ranar Litinin, ya ce nasarar zabe alama ce da ke nuna cewa Erdogan ya ci gaba da rike cikakkiyar amanar al’ummar Turkiyya.
- Da Dumi-dumi: An Rantsar Da Tinubu A Matsayin Shugaban Nijeriya Na 16
- Kotu Ta Ci Tarar Wadanda Suka Yi Karar Dakatar Da Rantsar Da Tinubu N17m
Tunibun ya kara da cewa yana fatan samun hadin kai tsakanin Nijeriya da Turkiyya.
Tinubu ya rubuta cewa: “Ina taya Shugaba Recep Tayyip Erdoğan (@RTERdogan) murnar nasarar zaben da ya yi a baya-bayan nan, nasarar zaben wata alama ce da ke nuna cewa ya ci gaba da rike cikakkiyar amana da amincewar al’ummar Turkiyya.
“Ina yi masa fatan samun nasarar wa’adin mulki tare da fatan samun hadin guiwa tsakanin kasashenmu biyu.”