Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, murnar zagayowar ranar haihuwarsa a ranar 21 ga Oktoba, 2025, yana mai bayyana cewa har yanzu suna da kyakkyawar alaƙa da zumunci tsakaninsu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya taya iyalan Kwankwaso, da abokansa da magoya bayansa murna, yana jinjinawa gudunmawar da ya bayar ga ci gaban ƙasa a muƙaman daban-daban da ya taɓa rike wa.
- Kwankwaso Ya Gana Da Shugabannin NNPP A Kuros Ribas Don Tunkarar Zaɓen 2027
- Kwankwaso na Tattaunawa da Shugaban APC Nentawe A Shirye-shiryen Sauya Sheƙa
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa Kwankwaso, wanda ya taɓa zama mataimakin kakakin majalisar wakilai a jamhuriya ta uku, da gwamnan Kano sau biyu, da ministan tsaro, da kuma sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ƙasar nan.
Tinubu ya ce shaharar Kwankwaso a Arewacin Nijeriya musamman a Jihar Kano ta nuna irin tasirin siyasa da kishin jama’a da yake yi, wadda ta yi kama da siyasar Marigayi Malam Aminu Kano da ta Marigayi Alhaji Abubakar Rimi.
Ya ƙara da cewa, “Sanata Kwankwaso aboki ne kuma abokin aiki, mun taɓa zama tare a majalisar dokoki a 1992, kuma dukkanmu mun zama gwamnoni a 1999. Mun kuma yi aiki tare wajen kafa jam’iyyar APC, duk da cewa daga baya ya kafa NNPP, har yanzu yana cikin sahun masu tunani na ci gaba.” Shugaban ƙasar ya yi masa fatan lafiya da ƙarin shekaru masu albarka wajen bauta wa ƙasa.