Shugaba Bola Tinubu ya taya Nafisa Abdullahi Aminu, Rukayya Muhammad Fema, da Hadiza Kashim Kalli kan murnar lashe gasar ilimi ta duniya a fannin fasahar sadarwa da muhawara a gasar TeenEagle Global na shekarar 2025 a birnin Landan na kasar Birtaniya.
Nafisa mai shekaru 17 a duniya, ita ce ta zama gwarzuwa a cikin fasahar harshen Ingilishi gaba daya; Rukayya ‘yar shekara 15 ta fito a matsayin wadda ta fi kowa iya muhawara, yayin da Hadiza ta lashe kyautar gwana (kambun zinare).
- Sin Ta Samar Da Yuan Biliyan Daya Domin Ayyukan Jin Kai Sakamakon Ibtila’in Ambaliyar Ruwa
- Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, shugaba Tinubu ya yabawa wadannan jiga-jigan matasan Nijeriya kan wannan bajinta tare da tabbatar da cewa makomar kasar nan tana da haske inda da yawa daga cikin matasanta ke taka rawar bajinta a duniya baki daya.
Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya.
Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi ne kawar da matsalolin kudi ga ‘yan Nijeriya marasa galihu da ke neman manyan makarantu ta hanyar ba su ba shi a ashirin Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp