Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarni ga dukkanin ma’aikatun gwamnatin tarayya da su daina sayen kayan da ake sarrafawa daga waje.
Wannan matakin na zuwa ne bayan amincewar da majalisar ministoci ta yi da sabon tsari na amfani da kayayyakin cikin gida a duk harkokin gwamnati.
- Zhao Xintong Ya Zamo Dan Nahiyar Asiya Na Farko Da Ya Lashe Gasar Snooker Ta Kasa Da Kasa
- Korar Ma’aikata: Likitocin Birnin Tarayya Sun Tsunduma Yajin Aikin Gargadi Na Kwanaki 3
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya shaida wa manema labarai bayan taron majalisar da aka gudanar a ranar Litinin cewa shugaban ƙasa zai rattaba hannu a kan wani umarni da zai tilasta amfani da kayayyakin da ake sarrafawa a Nijeriya.
Ya ce daga yanzu, babu wani kaya ko na’ura da ake iya samar da su a cikin gida da za a sake shigo da su daga ƙasashen waje sai dai da cikakken dalili.
Ministan ya bayyana cewa wannan tsari zai taimaka wajen tallafa wa masana’antun cikin gida, ƙara yawan ayyukan yi, da kuma inganta tattalin arziƙin ƙasa.
A cewarsa, gwamnati za ta mayar da hankali wajen sauya yadda ake kashe kuɗaɗe da kuma yadda ake gudanar da saye da sayarwa, ta yadda hakan zai amfani jama’a da ƙasar baki ɗaya.
Tsarin zai shafi duk wasu kaya da ma’aikatu ke amfani da su, kama daga kayan ofis, na’urorin zamani, kayan aikin gini da sauran su.
Ana kuma sa ran wannan mataki zai rage dogaro da ƙasashen waje, da kuma bai wa kamfanonin cikin gida damar bunƙasa tare da samar da guraben ayyukan yi ga matasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp