Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, murna bisa ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa mai suna ‘Being True to Myself’, wanda aka yi a yau.
Shugaban Ƙasa ya bayyana littafin a matsayin muhimmin ƙari ga tarihin siyasar Nijeriya.
- Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja
- Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasar a wajen taron da aka gudanar a Cibiyar Taro ta NAF da ke Abuja, ya bayyana Lamiɗo a matsayin ɗan siyasa jarumi kuma mai aƙida wanda tafiyar rayuwar sa ta yi daidai da cigaban dimokiraɗiyyar Nijeriya.
Idris ya ce: “Wannan ba kawai ƙaddamar da littafi ba ne, amma bikin rayuwa da jarumtaka, daidaito, da jajircewa ga tsarin dimokiraɗiyya suka bayyana.
“Ko da yake Alhaji Sule Lamiɗo babban jigo ne a jam’iyyar adawa kuma sau da dama mai suka ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), har yanzu yana daga cikin manyan ginshiƙai na cigaban siyasar Nijeriya.”
Ministan ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya yarda da siyasar da ke bai wa kowa dama, inda ake maraba da ra’ayoyi mabanbanta, kuma suna da muhimmanci ga tattaunawa kan makomar ƙasa.
“Kowane ɗan ƙasa, ba tare da la’akari da dangantakar sa da jam’iyya ba, yana da gurbin zama a teburin tattaunawa kan makomar ƙasa.”
Idris ya jinjina wa ƙoƙarin da Lamiɗo ya yi na fiye da shekaru goma wajen rubuta littafin, yana mai cewa ya taka rawar gani wajen adana tarihi, kuma ya buƙaci sauran tsofaffin ‘yan siyasa da su bi irin wannan hanya.
Ya kuma ce taken littafin, wato ‘Being True to Myself,’ ya dace da halayen Lamiɗo.
Ya ce: “Ya dace da halin Sule Lamiɗo da kuma sunan da yake da shi na ɗan siyasa mai aƙida da nuna ra’ayi kai-tsaye.
“Zan shawarci ɗalibai, malamai, ‘yan jarida, da sauran ‘yan siyasa da su karanta littafin don za su ga littafin yana da amfani a gare su na tsawon shekaru.”
Idris ya ƙara da cewa shi ma Shugaba Tinubu, kamar Lamiɗo, ya jajirce kan gaskiya, adalci, zaman lafiya da cigaban ƙasa.
Ya ce: “Ɗimbin ilimi da ƙwarewar marubucin, tabbas, wata baiwa ce da ya kamata duniya ta amfana da ita, kuma abin farin ciki ne ganin ya ɗauki mataki ya wallafa littafi.”
Yayin da Nijeriya take shirin cika shekaru 26 da dimokiraɗiyya, ministan ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa – duk da yake masu tsauri ne – sun fara haifar da sakamako mai kyau a fannin tattalin arziki.
Ya ce: “Shin muna cewa mun kai inda ya kamata mu kai, kuma babu sauran aikin da ya rage? A’a, ko kaɗan. Abin da muke cewa mai sauƙi ne: cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna ƙarfin hali da hangen nesa na musamman wajen ɗora Nijeriya a kan hanyar cigaba da bunƙasa na gaskiya.
“Kuma, bayan wata farawa mai ɗan wahala saboda tsauraran sauye-sauyen da ba za a guje masu ba, yanzu muna shiga wani sabon zamani na samun sakamakon alheri da aka yi niyya.”
Game da matsalar tsaro, ministan ya tabbatar da cewa Shugaban Ƙasa yana aiki tuƙuru wajen kare rayuka da ƙasa daga barazanar ‘yan ta’adda.
“Don haka muna son jaddada buƙatar a yaba da sadaukarwar da sojojin Nijeriya suke yi a wannan fanni,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa sababbin dokokin haraji da Shugaban Ƙasa ya gabatar suna nufin haɓaka kuɗaɗen shiga ga gwamnatoci a matakai daban-daban ba tare da ƙara wa talakawa nauyi ba.
“Shugaban Ƙasa yana maraba da suka mai ma’ana a kowane lokaci, cikin ruhin ’yancin faɗar albarkacin baki da dimokiraɗiyya, amma ba zai taɓa bari a karkatar da shi daga aikata abin da ya dace da Nijeriya ba.”
Manyan baƙi daga bangarori daban-daban na siyasa sun halarci taron don girmama tsohon gwamnan da kuma yin nazari kan gudunmawar da ya bayar wajen gina dimokiraɗiyya a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp