Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gayyaci kasashen duniya, musamman na Nahiyar Afirka da su garzayo don amfani da damar zuba jari, domin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Wannan dalili ne ya sa, shugaban ya roki Sojojin Ruwan Nijeriya da abokan huldarsu na Afirka da kuma sauran masu ruwa tsaki; da su mayar da hankali wajen ci gaba da inganta harkokin wannan fanni da ya shafi tashoshin jiragen ruwan wannan kasa, wanda kowa da kowa zai iya cin gajiyarsa, shugaban ya kara da cewa; Nijeriya ba za ta taba gazawa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na Afirka da ma duniya baki-daya ba.
- Hanyar Ci Gaba Da Gwamnatin Tinubu Za Ta Bi, Ba Takure Tunani Wuri Guda Ba – Obasanjo
- Da Dumi-Dumi: Edun Ya Mika Wa Tinubu Sabon Tsarin Mafi Karancin Albashin Ma’aikata
Tinubu ya yi wannan kira ne a lokacin bikin bude taron kasa da kasa na shekarar 2024, wanda aka gudanar a tashar jiragen ruwa da ke Jihar Legas.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne ya wakilce shi a wajen taron, a wata sanarwa da mai taimaka wa Mataimakin Shugaban Kasar kan harkokin yada labarai, Stanley Nwkocha ya fitar inda yake cewa, Shugaba Tinubu ya lura duk da cewa; bunkasar tattalin arziki shi ne ginshikin ci gaban kowace kasa; don haka, hanyar kadai da za a bi a samu wannan bunkasar tattalin arziki ita ce, “idan har kasa tana da jajurtattun sojojin ruwa.”
Daga nan, sai ya nemi kara kwazo da sadarwar hafsoshin sojojin ruwan Nijeriya da kuma na kasashen waje, inda ya bayyana su a matsayin “dakaru masu kula da harkokin teku.”
A cikin jawabinsa mai taken, “Lokaci ya yi da za mu tabbatar da kare Tekunmu”, wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Shettima ya karanta; inda yake shaida wa taron cewa, wajibi ne wannan taro ya zaburar da dukkanin wani mai ruwa da tsaki, don ganin ba mu yi kasa a gwiwa ba a kan dukkan abin da ya shafi ayyukan nahiyarmu da ma sauran dukkanin duniya baki-daya.
“Saboda haka, ya zama lallai mu himmatu wajen ci gaba da tsare wannan Teku, domin wadata da kuma dorewar amfanuwa da ita ga dukkanin al’ummar wannan kasa na yanzu da ma wadanda za su zo a nan gaba. Har ila yau, ina rokon ku da ku saki jiki; ku yi amfani da wannan dama, wajen zuba jarinku kamar yadda za ku yi a naku kasashen; don bunkasar tattalin arzikin wannan kasa Nijeriya.”
Ya kara da cewa, mahalarta wannan taro na da rawar da za su taka a yunkurin da ya yi na kokarin sake habaka tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar teku, wanda a duk shekara ya kayyade dala tiriliyan 1.5 a bangaren da ya shafi duniya baki-daya da kuma dala biliyan 300, a bangaren Afirka; Shugaba Tinubu ya ce; ba za a taba samun wadataccen arziki a Afirka ba, har sai an mayar da hankali tare da bunkasa yanayin wannan Teku namu.
Har ila yau, “An kiyasta cewa, darajar tattalin arzikinmu a duniya zai rika bunkasa tare da kai wa kimanin dalar Amurka tiriliyan 1.5 a duk shekara, sannan ana hasashen zai karu zuwa dala tiriliyan 15.5 nan da shekarar 2050.
Kazalika, “Tsarin tattalin arzikin Afirka ta hanyar mayar da hankali kan Teku, an kiyasta za a iya samar da kimanin dalar Amurka biliyan 300 ga nahiyar tare da samar da ayyukan yi kimanin miliyan 49. Haka nan kuma, an yi hasashen tattalin arzikin Afirka ta hanyar Teku; zai sake bunkasa da kimanin dalar Amurka biliyan 405 nan da shekarar 2030,” in ji shi.
Har wa yau, Shugaban Kasar ya taya Sojojin Ruwan Nijeriyar murnar cika shekara 68 da kafuwa, yana mai cewa; al’ummar kasar nan na ci gaba da nuna godiya ga hidimar da suka yi a cikin wadannan shekaru 68, “a matsayinku na masu tsaronmu da kuma tsaron al’amuran da suka shafi teku, wajibi ne a yaba muku da wannan kokari kwarai da gaske a cikin wannan kasa”.
Haka nan, musamman shugaban ya yaba wa Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle; Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Bice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla, da sauran hafsoshin ruwan; sakamakon samar da tsaro tare da ci gaba, don bunkasar tattalin arzikin wannan kasa.
“Babban abin da za mu mayar da hankali a kai shi ne, tabbatar da samar da kayayayakin more rayuwa da sauran ingantattun kayayyakin aiki masu inganci ga Hafsoshin Sojojin Ruwa, wadanda suka hada da makaman yaki na zamani; domin kuwa za mu iya tunawa da nasarar da suka samu wajen dakile hana satar danyan mai; tun bayan shigowarmu wannan gwamnati a shekarar 2023. Babu shakka, wannan ya yi matukar ba da gudunmawa sosai ga karuwar samar da danyan mai kamar yadda muka gani,” in ji shi.
Tun da farko, a jawabinsa na maraba; Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Ruwa, Bice Admiral Ogalla ya ce; wannan taro na kasa da kasa da aka shirya a wannan shekara ta 2024, an shirya shi ne don tuna wa da cika shekara 68 da kafuwar Sojojin Ruwan Nijeriya, sannan zai taimaka kwarai wajen inganta karfinsu da kuma karfafa hadin gwiwar da ake da ita wajen kare al’ummar kasa da kuma yankunan Teku a halin yanzu.
Ya kara da cewa, dandalin zai kuma bayar da dama wajen karfafa irin nasarorin da hadin gwiwar Rundunonin Sojojin Ruwa za su bayar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa a nahiyar da ma kuma kasa baki-daya.
A nasa bangaren, Karamin Ministan Tsaro Matawalle; ya bukaci mahalarta taron da kuma sauran abokan huldar Sojojin Ruwan Nijeriya, da su fito da wasu sabbin hanyoyi wadanda sojojin ruwan yankin za su iya amfana da su, ta yadda Nijeriya za ta iya aiwatar da manufofinta; ba tare da samun wata tangarda ba, haka nan; Nijeriya ba za ta iya aiwatar da manufofin da take son gudanarwa ba, har sai Shugaba Tinubu ya tabbatar da inganci tare da tsaron yankunan wannan Teku.
Haka zalika, Mataimakin Gwamnan Jihar Legas Mista Obafemi Hamzat, yayin da yake yaba wa da gagarumin ci gaban da Sojojin Ruwan Nijeriyar suka samu, musamman wajen kare martabar yankunan Tekun kasar, ya ce taron ya baje kolin kayayyakin tarihi na kasar da kuma kokarin da Sojoji Ruwan Nijeriyar ke yi a Tekun kasar.
Bugu da kari, a lokacin da Mataimakin Shugaban Kasar ya isa tashar jiragen ruwan, ya kaddamar da wasu sabbin jirage guda uku da ake yi wa lakabi da; OCHUZO, CHALAWA, ZUR, dukkaninsu mallakar Sojojin Ruwan da kuma wasu jiragen masu saukar ungulu guda biyu.
Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, wanda ya wakilci Shugaban Kasar, daga bisani ya ci gaba da ayyana bude atisayen jiragen ruwa na yaki tare kuma da duba aikin da ake gudanarwa na jiragen sojojin ruwan da ke lardin Tekun.