Rukunin kamfanin LEADERSHIP ta shelanta zabar Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a matsayin gwarzon shekarar 2023.
A wata sanarwar da kamfanin ta fitar dauke da sanya hannun shugaba, Zainab Nda-Ishaih a ranar Litinin, ta ce LEADERSHIP, ta zabi Tinubu ne saboda yadda ya jajirce ya dage wajen tsallake tulin kalubalen da suke gabansa a ciki da wajen jam’iyyarsa ta APC har ya zama halastaccen shugaban kasar Nijeriya a zaben watan Fabrairun 2023.
- Tinubu Ya Sake Mika Ta’aziyyarsa Ga Iyalan Da Harin Bam Ya Rutsa A Tudun Biri, Kaduna
- Muna Fata Masu Talla A Kafafen Sada Zumunta Su Fadakar Kan Shirye-shiryen Tinubu Na Habaka Tattalin Arziki
Sanarwar ta kuma yi nuni kan irin salon matsayar da Tinubu ya dauka duk da tulin wahalhalun da suke akwai musamman jim kadan bayan darewarsa karagar mulki na yunkurinsa na sake farfado da Nijeriya.
Bikin gabatar da lambar karramawa ta LEADERSHIP, na gudana ne a yayin babban taron mika lambar yabo da jawabai na LEADERSHIP, kuma wannan shi ne karo na 16 da jaridar ke gudanarwa. Kan hakan, ana zakulo jajirtattun ‘yan Nijeriya, hazikan ma’aikata, daidaiku, da kamfanonin da suka yi zarra a bangarori daban-daban domin karrama su.
Tsarin zabin wadanda za su amshi lambar yabon ya gudana ne a watan Nuwamba wanda manya-manyan jagororin (majalisar editoci) na jaridar da sashin kasuwanci hade da manbobin hukumar ba da shawarwari wadanda kwararru ne a bangarori daban-daban suka cimma.
Tinubu ya kasance tsohon sanata, gwamnan farar hula har na wa’adi biyu a Jihar Legas, kuma ya amshi lambar yabon LEADERSHIP sau biyu, ya taka gagarumar rawa wajen samun nasarar APC wanda hakan ya kawo karshen mulkin PDP na shekaru 16, inda APC din ta kwace ragamar a 2015.
Duk da rawar da ya taka, ya sha gwagwarmaya a jam’iyyar na tsawon shekara takwas daga bisani ya yi kukan kura har ya samu nasarar jan ragamar komai na jam’iyyar da ma kasar nan baki daya.
A lokacin da ya shelanta aniyarsa na fitowa takara, Tinubu ya fuskanci tirjiya da koma baya daga cikin jam’iyyarsa ciki har ma da jami’an gwamnati a wancan lokacin da aka yi ta kawo abubuwan da za su iya zame masa tarnaki ga samun nasarar zama shugaban kasa ciki, wanda suka hada da rikita-rikitar canza fasalin takardun kudi da aka yi domin dakile aniyarsa na zama shugaban kasa.
Daker gwamnatin Muhammadu Buhar ta hakura ta amince ta mara masa baya har zuwa lokacin da gwamnonin APC na arewa suka tursasa gwamnatin da a mika ragamar takarar Nijeriya zuwa ga yankin kudancin kasar nan.