Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai gana da zababbun Sanatoci da zababbun ‘yan majalisar wakilai dangane da shugabancin majalisar tarayyar Nijeriya a gobe Alhamis.
Sanarwar ganawar ta fito ne a cikin wata wasika da aka aike wa majalisar kuma mataimakin shugaban majalisar, Ovie Omo-Agege wanda ya jagoranci zaman a ranar Laraba ya karanta.
Wasikar tana cewa: “Ina amfani da wannan kafar ina gayyatar dukkan zababbun Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai a fadar gwamnati a ranar Alhamis 8 ga watan Yunin 2023 da karfe 2 na rana.”
Duk da cewa, ba a bayyana dalilin gayyatar ba a cikin wasikar, amma majiyoyi sun ce, ganawar ba za ta rasa nasaba da shugabancin majalisar ta 10 ba.
A baya dai jam’iyyar APC ta amince da tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio da Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Barau Jibrin a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa.
A majalisar wakilai, Hon Tajudeen Abbas da Ben Kalu su jam’iyyar ta amince a matsayin kakakin majalisar wakilai da mataimakinsa.
Sai dai tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, da shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Orji Kalu, Osita Izunaso da Sanata Sani Musa sun hada kai kan yi wa zaben jam’iyyar tawaye.