Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai karrama mahajjaciyar ‘yar asalin Jihar Zamfara, Hajiya Aishatu ‘Yan Guru Bungudu Nahuche, wacce ta tsinci Dala 80,000, kwatankwacin naira miliyan 60 ta mayar a lokacin da gudanar da aikin hajjin bana a kasa mai tsarki.
Shugaban kwamitin aikin hajji na Jihar Zamfara, Alhaji Musa Mallaha ya bayyana hakan a lokacin taron manema labarai da ya gudana a ofishinsa. Ya kara da cewa shugaban kasa ya yi matukar murna da faruwar lamarin wanda tuni ya umarci hukumar jindadin alhazai ta kasa ta shirya taron manema labarai na kasa kan wannan mata domin karrama ta da kuma ajiye bayanai.
“A daidai lokacin da hukumar ta tuntube mu, matar tana cikin jirgi za ta koma Nijeriya bayan kammala aikin hajji.
“A yanzu haka muna tattaunawa da gwamnanmu na Zamfara domin ya kasance daga cikin bikin karramawar da matar gwamna za ta a yi wa wannan mata,” in ji Mallaha.
Mallaha ya bayyana jin dadinsa bisa wannan karanci da dabi’u na kwarai da wannan mahajjaciya ta nuna. Ya ce wannan kyawawan dabi’u da ta nuna ba wai ya daga darajar Jihar Zamfara kadai ba har ma da Nijeriya da kuma dukkan kasashen Musulmin duniya gaba daya.
“Dabi’un kirki na daya daga cikin koyarwar Alkur’ani wanda yana daga cikin ka’idojin Musulunci,” in ji shi.