Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar dokoki takardar neman amincewarta domin ciwo bashin m kudi dala biliyan 8.69 da kuma Fam miliyan 100.
Shugaban ya ce za a yi amfani da lamunin ne wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka da suka hada da wutar lantarki da hanyoyi da ruwan sha da hanyoyin jiragen kasa da kuma kiwon lafiya.
- NNPP Ta Nemi EU, Amurka Da AU Su Kawo Mata Dauki Kan Zaben Gwamnan Kano
- OECD: Gdpn Sin Zai Karu Da Kashi 5.2 A 2023
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, sun gabatar da wasikar ta shugaban kasa ga ‘yan majalisar.
Wannan neman lamunin dai kari ne kan neman hurumin karbo lamuni da Tinubu ya yi a baya da majalisar ba ta kai ga amincewa da shi ba.
Wasikar da Tinubu ya aike a baya, ta kunshi neman lamunin dala biliyan 7.86 da kuma Fam miliyan 100.
Takardar ta nuna wannan na daga cikin tsarin cin bashi na shekara ta 2024 mai shigowa.
A a ranar Laraba ne dai Tinubu ya gabatar da kasafin kudin ga majalisar dokoki.
A zamanin gwamnatin Buhari, kasafin kudin Nijeriya ya dawo aiki daga watan Janairu zuwa Disamba.
Idan ba a manta ba, gwamnatin baya ta Muhammadu Buhari, tafi kowace gwamnati a tarihin Nijeriya cin bashi, da hakan ya nuna yanzu zaba jira a ga zuwa karshen mulkin Tinubu ko zai iya zarce Buhari ko kuma a samu akasin haka.