Shugaba Bola Tinubu da kansa zai sanar da sabuwar ranar da za a gudanar da kidayar jama’a da gidaje da aka dage a watan Afrilun da ya gabata.
Shugaban hukumar NPC na kasa, Nasir Kwarra, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan tawagarsa ta yi wa shugaban kasa cikakken bayani a Fadar Aso Rock Villa da ke Abuja ranar Alhamis.
- Tinubu Zai Sanya Lokacin Da Za A Yi Kidayar 2023
- Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Dage Kidayar Jama’a Zuwa Watan Mayun 2023
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta mika rahotonta ga shugaban kasa, wanda ake sa ran zai yi nazari tare da yanke shawarar lokacin da za a gudanar da aikin kidayar a fadin kasa.
Ya kuma yi nuni da cewa akwai yuwuwar hukumar ta kara bijiro da bukatun samar mata da karin kudaden gudanarwa, yana mai cewa idan aka dade ana jinkirin aikin, zai iya kara yin tasiri a kan kudin gudanar da aikin.
“Mun bayyana masa (Tinubu) dalla-dalla kan matakin shirye-shiryenmu, sakamakon da muke hasashen kuma ina so in ce shugaban kasa ya amince da tallafa wa hukumar wajen gudanar da kidayar jama’a da ayyukanmu na shirye-shirye, ya bamu ƙarfin guiwa kan shirye-shiryenmu.
“Don haka za mu ci gaba da shirye-shiryenmu kuma za mu ji ta bakinsa daga karshe, ranar da za a yi kidayar jama’a saboda mun mika masa cewa zai yi nazari kafin ya dawo gare mu.
“Amma dangane da tabbacin goyon bayansa, kuma muna gode masa matuka saboda wannan ya fahimci mahimmancin tsare-tsare da ci gaban kasa,” cewar Kwarra.