Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tarbu gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Jihar Katsina a yau Talata.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ne ya tabbatar da haka a ranar Litinin da yamma a Abuja.
- Na Yafe Wa Buhari Duk Abin Da Ya Min – Buba Galadima
- Sarkin Maroko Ya Aike Da Ta’aziyya Ga Nijeriya Bisa Rasuwar Buhari
A cewar ministan, za a kawo gawar Buhari zuwa Katsina da misalin ƙarfe 12 na rana, inda za a yi masa faretin ban girma a filin jirgin saman Katsina.
Daga nan ne kuma za a tafi da gawarsa zuwa garinsu Daura domin yin jana’iza.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, yana Landan a halin yanzu, kuma shi ne zai taho da gawar Buhari zuwa Katsina.
Gwamnatin Tarayya ta riga ta kafa kwamitin da zai shirya duk abubuwan da suka shafi jana’izar, ciki har da shirin binne tsohon shugaban ƙasar.