Tsohon mataimain shugaban kasar Nijeriya, Atiku Abubakar, ya roki jiga-jigan ‘yan adawa, Peter Obi, da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ‘yan takaran shugaban kasa a zaben 2023 na jam’iyyar LP da NNPP bi da bi domin su hada karfi da karfe wajen tabbatar da gaskiya kan tirka-tirkan takardun Tinubu.
Abubakar wanda ke magana dangane da sakamakon karatun da jami’ar Chicago ta fitar dangane da shaidar karatun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, inda ake ta samun tirka-tirka kan lamuran.
- Tattalin Arzikin Afirka Zai Durkushe – Bankin Duniya
- Ambaliyar Ruwa Ta Raba Mutane 563 Da Muhallansu A Adamawa
“Ya ku ’yan uwana na Tarayyar Nijeriya, ya dace in yi tsokaci kan batutuwan da suka fayyace makomar zababbun gwamnati da halastaccen shugabanci a kasarmu (Nijeriya).
“Shugabancin siyasa da zama dan kasa na da matukar muhimmanci, domin su ne hanyoyin da muke hada kai don gina kasa mai aminci ga duk wanda ke zaune a cikinta. Kasarmu ta fi girman kowannenmu, kuma matsayinta a duniya yana shafar makomar duk dan cikinta – wanda ya fita ketare ko kuma yake zaune a cikinta. A matsayinmu na shugabanni, ya zama wajibi mu ci gaba da kyautata rayuwar al’ummarmu da kasa baki daya.
“Don haka ne, shugabannin da suka riga mu suka yi aiki tukuru wajen mayar da sojoji bariki da kare hakkin jama’a na yij zabe da kafa wa kanmu halastacciyar gwamnati. Zaben mu an kafa shi ne bisa doka kuma an kafa shi bisa tsarin mulki ta yadda za a samu halastacciyar gwamnati.
“Jama’a suna kallon mu a matsayinmu na shugabanni don mu mutunta wadannan dokoki kuma mu kare su. Wannan shi ne ya tara mu a nan.
“Wannan tafiyar da nake nema a gareku, ba don bukatata (Atiku Abubakar) ce kawai ba; tafiya ce ta tabbatar da halastacciyar gwamnati, tabbatar da gaskiya, adalci, da rikon amana a cikin al’amuranmu,”
“A bisa wannan, ina yin kira ga dukkan ‘yan Nijeriya masu kishi, shugabanninmu masu tunani, shugabannin addini da gargajiya, al’umma, da shugabannin siyasa.
“Musamman, Peter Obi na Jam’iyyar (LP), Rabi’u Kwankwaso na NNPP, shugabannin jam’iyyun siyasa a Nijeriya, da duk wani mai kishin kasar nan kamar ni, wanda ba ya fatan komai sai alheri ga kasar nan da ya hada hannu da mu cikin wannan aiki – yakin neman tabbatar da adalci da gaskiya a cikin kasarmu da gwamnatinmu.” Inji Atiku