Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta doke abokiyar karawarta Manchester United da ci daya mai ban haushi a wasan karshe na gasar Zakarun Turai ta UEFA Europa League a filin wasa na San Mames dake Bilbao.
Wannan shi ne karo na uku da Tottenham din ta lashe kofin Zakarun Turai na Europa bayan ta lashe a shekarun 1971 da 1983 ta kuma kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai a shekarar 2019 inda Liverpool ta doke ta.
Manchester United ta rasa damar buga gasar Zakarun Turai ta badi bayan wannan rashin nasarar da tayi, wannan ne karon farko da United din ta yi rashin nasara a wannan gasar a bana.
Duka kungiyoyin biyu sun kasa tabuka abin azo agani a wannan kakar a gasar Firimiya Lig, inda Manchester United ke matsayi na 16 Tottenhma na bi mata, amma wannan nasarar da yaran na Postecoglu suka samu ya sa sun samu gurbi kai tsaye a gasar Zakarun Turai ta badi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp