Matashiyarmu ta wannan Sati mai taken “Tozon Basuka A Jihohin Kano Da Kaduna”, ita ce za ta mayegurbin waccan matashiya tamu ta Makon da ya gabata, wato “Rumbun Basuka A Jihohin Kano Da Kaduna”. Kamar yadda aka yi ishara cikin rubutun da ya gabata cewa, yanzu haka za mu gangaro ne sannu a hankali cikin jihohin wannan Kasa daya bayan daya, don gano irin nasu sha’anin saki na dafen da suke yi wa harkar kandamo basuka a cikin gida da ketare.
El-Rufa’i Da Basuka A Kaduna
A can can baya cikin wannan rubutu, an dan fara hakaito wani abu daga irin basukan da gwamna El-Rufa’i ya ciwowa jiharsa ta Kaduna, daga wani sakamakon bincike da mutane irinsu Daniel Ayantoye da Ayoola Olasupo da John Charles da kuma Nwakanma suka fitar, a ranar 25 ga Watan Mac na Shekarar 2023 (March 25, 2023), mai taken ” 17 Gobernors To Inherit N 2.1trn, $ 1.9bn Debts”, inda aka ankarar da cewa, tsibirin basukan da gwamna El-Rufa’i ya samar a jihar ta Kaduna, ya kere daukacin dandazon basukan da jihohi tara a wannan Kasa (9) suka ciwowa jihohinsu bakidaya.
Babu shakka ga wanda ya bibiyi ta’adar gwamna El-Rufa’i game da irin nau’in basukan gida da na daji da yake kandamowa al’umar jihar Kaduna, a na iya sanya shi a sahun wasu gwamnonin da ke da wata halaiya iri biyu, game da taragon basukan da a kullum suke jibgewa jama’ar da suke mulka, ba tare da yin karatun ta natsun alkaba’in da ka je ya zo ba. Sama da kashi tamanin (80%) na basukan da gwamnatin Kaduna ke hadiya a karkashin Nasiru, ba a sanya su cikin irin aiyukan da masana tattalin arzikin Kasa ke goyon bayan a sanya kudaden da aka ciwo bashi cikinsu.
“…The new gobernors would face some challenges with the debts burden, such could be minimised if strong economic and financial teams were put in place…”
“…If the outgoing gobernments inbested the loans in productibe inbestments and projects, the state would be able to generate funds to serbice the debts and fund other projects”
Joseph Babatunde
Wadancan kalamai da aka gabatar a sama cikin harshen Ingilishi da masanin tattalin arziki kuma tsohon babban manajan manyan Masana’antu hade da Bankin na Masana’antu ya fada, na yin ishara ne zuwa ga matsalolin da ciwo irin wadancan basuka ke haifarwa ga Kasa, tare da gabatar da hanyoyin magance su. Zai yi matukar alfanu, a dan fassara wadancan kalaman Turanci zuwa Hausa gwargwado. Ga abinda suke cewa;
“…A fili ne yake cewa, sabbin gwamnoni da aka zaba za su fuskanci manyan kalubale da kuma wahalhalun da irin wadancan basuka da aka ciwo ke haifarwa. Kadai, za a rage irin wadannan wahalhalu ne ta hanyar samar da wasu kunshin masana tattalin arzikin Kasa na gaske kuma a aikace, kuma masana sauran huldodin kudade…”.
“…Da a ce gwamnonin da suka kare wa’adin mulkinsu sun sanya hannun jari na irin wadancan basuka da suka ciwo, a cikin hannayen jarin da za su hayaiyafa, ko a ce sun sanya su ne cikin wasu aiyukan da suma za su haihu, to da babu shakka gwamnati na iya samun madudan kudaden shigar da za su taimaka zuwa ga biyan wadancan basuka, sannan a daya hannun kuma, su agaza zuwa ga daukar nauyin samar da wasu aiyuka na ci gaba ga al’umar Kasa”.
Dambarwar Sani Da El-Rufa’i Ga Batun Ciwo Bashi A Kaduna, 2017
Gabanin jihar Kaduna ta ciwo kwallo a matsayinta na jihar da duk cikin daukacin jihohi 17 da sabbin gwamnoni za su karbi rantsuwar kama aiki a cikinsu, a ranar 29 ga Watan Mayun Shekarar da muke ciki ta 2023, ta kere kowace jiha yin tatul ko a ce yin hani’an da tulin basukan gida da na waje na malala gashin tinkiya. Ta tabbata, Shekaru shida da suka gabata (2017), tuni gwamna El-Rufa’i ya nuna tsananin sha’awarsa ga son ciwo tarin basukan da ga dukkan alamu har lokacin da zai koma zuwa ga Mahaliccinsa, jihar ba za ta iya biyan jogogon basukan da ya rikito mata ba!.
Idan za a iya tunawa, cikin Shekarar 2017 ne aka dinga samun wani zazzafan kiki-kaka da kuma tsananin rashin fahimtar juna a tsakanin gwamna Nasiru El-Rufa’i da Sanata Shehu Sani, game da lamarin dibgowa jihar basuka daga ketare da gwamnan ya tubure sai ya yi, inda Sanatan ya lashi takobin atafau ba za ta sabu ba bindiga a ruwa.
Daga cikin hujjoji da Sani ke bijirarwa na rashin yardarsa ga gwamna wajen ciwo bashi daga kasashen waje shi ne, ta tabbata tun daga lokacin da Najeriya ta samu ‘yancin kai daga turawan Birtaniya, 1960, zuwa Shekarar 2017, dalar Amurka miliyan dari biyu ($200m) ne kacal ake bin jihar ta Kaduna bashi. Amma sai ga El-Rufa’i ya tubure fafur da rana tsaka sai ya ciwowa jihar Kaduna bashin zunzurutun kudade har kimanin dalar Amurka miliyan dari uku da hamsin ($350m) daga Bankin Duniya. Bankin da, shi, da takwararsa na IMF, sun durkusar ta tarin kasashen mabanbantan nahiyoyin Duniya ta hanyar hambuda musu basukan shankai!.
A sama an fada cewa, daga Shekarar 1960 har zuwa 2017, an biyo jihar Kaduna bashin ketare ne da bai wuce dalar Amurka miliyan 200 ba, amma sai aka wayigari karkashin gwamnatin dimukradiyyar da jama’a ne ke da ikon sarrafa ta yadda suka so, kuma sai aka sami wani gwamna farar hula na neman jefa jihar zuwa ga ramin bashin da zai kusan ninka daukacin basukan da ake binta zuwa ga ribi ko ninki biyu. Ina dimukradiyya a nan? Wancan lokaci fa da aka ciwo dala miliyan dari 200, akasarin Shekarun lokacin, Sojoji ne ke mulkar Kasar, shi ne zamanin da ya kamata a fi ganin karfa-karfar masu mulki amma ba lokacin da jama’ar Kaduna suka fito tare da dora El-Rufa’i bisa kujerar mulki, don ya hidimta musu, amma ba don ya azabtar da su ba!.
Yadda a kullum El-Rufa’i ke nunawa jama’ar Najeriya shi mai kishin Kasa ne da al’uma, idan da gaske yake, yunkurin bin hanyoyin da za a rage yawan bashin ne ai zai lalubo, ba sake dankaro wasu basukan ba. Wani abin tsoro ga wannan bashin da El-Rufa’in ke son ciwowa, a tsarin biyansa, sai an shafe sama da Shekaru hamsin (50yrs) ne a na biyansa. Ina dalili ina dan mafari!!!.
Sanata Sani yake cewa, yanzu haka fa jihar tamu ta Kaduna na cuku-cukun biyan albashi ne a duk karshen Wata, sannan a hankali a hankali kuma jihar tana mirginawa ne wajen biyan shudaddun basukan da gwamnatocin baya suka ciwo mata. Ke nan, ba a ka da Gizo ba, sai ga Nasiru ya tasamma Koki!
Bugu da kari, wani yanayi na ban firgici game da ciwo basuka da jihar Kaduna ta afka karkashin mulkin Nasiru shi ne, an fadi cewa, Shekaru shida da suka gabata, an zargi gwamna Nasiru ne da yunkurin rikito bashin dalar Amurka miliyan dari biyu ne, to amma cikin Shekarar 2023, sai ga wani rahoton manazarta da ke hakkake cewa, an wayigari a yau, a na bin jihar Kaduna zunzurutun basukan waje, har na kimanin sama da dalar Amurka miliyan dari biyar da tamanin da shida ($ 586,776,219.18), wannan shi ake cewa, a na kukan targade, sai ga karaya ta samu!.
Kumbiya-kumbiya A Bashin Dala Miliyan Dari Uku Da Hamshin ($350m)
Babu shakka barewa ba tai gudu danta ya yi rarrafe ba, tamkar irin yadda aka gabatar a baya cewa, a wasu lokuta gwamnatin taraiya karkashin mulkin Baba Buhari kan yi wani dungushe wajen kin faiyacewa jama’ar Kasa hakikanin abin da aka nufata aikatawa da irin wadancan biliyoyin daloli da ake ciwo bashinsu daga angarar turawan yamma dare da rana, har ma wasu na kokarin nakaltawa shugaban gwamnati suna da BABA ACICI, saboda himmatuwarsa ga ciwo basuka na kudade malala gashin tunkiya, kuma ko sau guda ba a ji shi yana kokawa ga wawaken ramin basuka da wannan Kasa ke hara ba, lamarin da a karshen fim din ke tarwatsa tattalin arzikin Kasa tare da mika ikon tattalin arzikin Kasar ga al’umar yammacin Duniya, tamkar irin yadda ya faru a Kasashe irinsu Argentina, Zambia, Malawi da sauransu.
Sammakal tsakanin Buhari da Nasiru, ta fuskar hadidiyar basuka ido rufe, tare da yunkurin yin ‘yar burum burum ga al’umar Kasa, na waskatar da tunaninsu ga makudan basukan da gwamnatocinsu ke ciwowa. Sanata Sani ya zargi Nasiru da wata boyaiyiyar manufa tattare da tozon kogin basukan da yake kokarin rikitowa jiharsa ta Kaduna a Shekarar 2017.
“…The basis for loan presented to me was that, World Bank was gibing $350 million loan to Nasir for Institutionan Reform…
…It is not about hospitals or roads or schools, they said reform. What are you going to reform? Now, what he is telling the public is that, he wants to do roads, he wants to do hospitals…
…You want to reform, what are you reforming with $350 million? That is why we habe to be bery careful!!!”. Shehu Sani
Gabanin fassara wadancan kalamai na Shehu Sani zuwa ga harshen Hausa, yana da kyau mai karatu ya sani cewa, su wadancan mutane na yammacin Duniya da ke kwararo mana tekunan bashi na biliyoyin daloli, babu ruwansu ko da za a ciwo irin wadancan basuka ne, daga karshe shugabanni su cinye, ba tare da jama’ar Kasa sun amfana ba! Ba su damu da ankarar da shugabanninmu wajen zuba irin wadancan makudan kudade cikin sabgogin hannayen jarin da za su samar da kudaden da za mu biya basukan da muke rantowa daga gare su ba. Bilhasali ma, a kullum burinsu shi ne a sami wadanda za su rika zuwa tare da tsugunawa gabansu ne rike da kokon barar neman bashi. Za ma a ga sharuddan wa’adi na biyan kudaden ba su damu da sanya gajeren lokaci ba, suna so ne a dauwama cin bashin dimun da’iman. Su dankara muku tarin basuka, sannan a shirye suke kafin ku biya, su kara dankara muku wasu mamakon basukan. Sanannen abu ne ga masana cewa, irin yanayin da kasashen Turai da ‘yan kanzaginsu irinsu World Bank da IMF da Paris Club da makamantansu ke ba da bashi ga mabukata, ya yi kwabo da kwabo ne da tsare tsarensu na mulkin mallaka a kaikaice ga al’umar Duniya.
Ko a unguwarku, ko a kasuwa, don me yasa wanda ke binka bashi ke zama surukinka?. Ko a wata fahimtar addini, za ka iya fashin juma’a, muddin wanda ke binka bashi zai datse hanya ya ganka ya ci maka fuska, saboda wani bashinsa da ka hadiya! Nahiyarku guda, kasarku guda, jiharku guda, karamar hukumarku guda, unguwarku ma guda, yarenku guda kuma ma addininku guda da wani mutum da ke binka bashi, amma ya zame maka wani alakakai ko a ce kadangaren bakin tulu! To yaya ke nan lamarin zai kasance ga wasu mutane da ke binka bashi, wadanda ba ka hada dukkan wata dangantaka da su ba, kuma ka yi tsammanin samun wata sawaba daga gare su?.
Ga wasu abubuwa da Sanata Shehu Sani ke labartawa cikin wadancan kalamai da ya gabatar cikin harshen Ingilishi kamar haka;
“…Babbar hujjar da aka gabatar min da ita wajen ciwo wannan bashi (na dala miliyan 350) shi ne, Bankin Duniya ya bai wa Nasiru bashin dalar Amurka miliyan dari uku da hamsin ($350m) don yin gyara da kwaskwarima ga wasu bangarori na rayuwar al’uma…
…Ba fa a na magana ba ne cewa za a gina asibitoci da hanyoyi da kuma makarantu ba, a’a, kawai dai an ce yin kwaskwarima. To wai wane gyara ko kwaskwarima ne ake son yi da kudaden? Sai dai kuma yanzu daga baya gwamna na fada wa mutane cewa, yana so ne ya gina hanyoyi da kuma asibitoci da kudaden…
…Wai kana so ka yi kwaskwarima, wace kwaskwarima ce za ka yi da zunzurutun kudade har kimanin dalar Amurka miliyan 350? Saboda haka dole ne mu tashi mu kula mu sanya idanu cikin wadannan lamura!!!”.
To mai karatu dai ka ji irin kalaman da shi Sanata Sani ke cewa, mu dauki misalin wasu abubuwa biyu zuwa uku mu karkare da su, daga nan kuma sai mu leka zuwa ga jihar Kano ta Dabo cigari, suma mu dubi irin murdadddiyar wainar bashin da suke toyewa, wadda a na tsaka da toyawa ne sai sabon gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuntsurar da kaskon tuyar!!!.
Daga maganganun Sanata Sani, ya ce;
–Bankin Duniya ya bai wa Nasiru bashin ne don yin kwaskwarima ga wasu bangarori na rayuwar jama’a.
Ta yaya ne ma za a ce an ciwo bashin ketare kawai don a yi wata kwaskwarima? Wace irin kwaskwarima, alhali ma yin wasu gine gine da kudaden bashin kan jefa kasa cikin masifa! Ai irin wadannan basuka a na sanya su ne cikin aikace aikace da kuma huldodin da za su taimaka zuwa ga su hayaiyafa, su sauke nauyin bashin da mashaya jinnai suka dora musu. Sannan, niyyar da Bankin Duniya yai ikirarin bai wa Nasiru kudaden, sun nuna gaskiyar maganar da aka yi a baya cewa, wadanda ke ba da rancen irn wadancan kudade, ba su damu da wadanda ke karba su amfana su amfanar ba! Tun da ba da bashin a yau, na daga sabbin dabarun mallakar Duniya ne. Za a dan fahimci hakan ne, duba da ka’idoji da sauran sharuddan da ake gindayawa kafin ba da bashin, da kuma lokacin da wanda aka bai wa bashin ya gaza cika sharuddan biya.
In ban da ma shugabanni na tafiya ne da ka a wannan Kasa, ta yaya ne za a sami wani shugaban da zai ciwo mamakon daloli da sunan bashi har dala Amurka miliyan 350, amma wai ya buge yana fada wa mutanensa cewa zai gina hanyoyi ne da su? Ina gungun masana tattalin arzikin kasa da ke yin aiki karkashin Nasiru, wace shawara suka ba shi a lokacin da yake irin wadancan furuce furuce?. Maasha Allah! Yanzu haka cikin Kaduna da kewaye za a iya ganin tarin hanyoyi da gadoji da gwamna mai barin gado Nasiru El-Rufa’i ya yi, ga su nan birjik iya ganinka. To amma, wadanne tsarin aiyuka da hannun jari ne da gwamnatin ta gabatar wadanda za su rika biyan makudan basukan da gwamnatinsa ta ciwo a hankali a hankali? Sabanin haka, akwai ayar tambaya gundumemiya da za ta ci gaba da yin reto a birbishinsa tsawon rayuwa!